Bisa ga Imanin Addinin Musulunci, Annabi Ibrahim (Larabci: إِبْرَاهِيْمُ‎, romanized: ʾIbrāhīm, Arabic pronunciation: [ʔɪbraːˈhiːm]) Annabi ne kuma manzon Allah,[1][2] kuma Kaka ga Larabawa Isma'ilawa da Isra'ilawa.[1] Annabi Ibrahim ya bayar da babbar gudummuwa a matsayin misali na ban gaskiya cikin Yahudanci, Kiristanci, da Musulunci.[1]

Annabi Ibrahim
Annabawa a Musulunci
Bayanai
Jinsi namiji
Suna Abraham
Suna a harshen gida إبراهيم
Shekarun haihuwa 1810s "BCE"
Wurin haihuwa Ur (en) Fassara da Babylonia (en) Fassara
Lokacin mutuwa unknown value
Wurin mutuwa Hebron (en) Fassara
Uba Terah in Islam (en) Fassara
Mata/miji Sarah (en) Fassara da Hajara
Yarinya/yaro Ismail (en) Fassara da Ishaaq
Relative (en) Fassara Lot in Islam (en) Fassara da Jacob in Islam (en) Fassara
Sana'a Mai da'awa da manzo
Muƙamin da ya riƙe Annabawa a Musulunci
Wanda ya biyo bayanshi Lot in Islam (en) Fassara

A aƙidar musulmi, Annabi Ibrahim ya cika dukkan dokoki da jarabawowin da Allah (SWT) ya raya shi a tsawon rayuwarsa. A sakamakon bangaskiyar da yake da ita ga Allah, Allah ya yi wa Annabi Ibrahim alkawari cewa zai zama shugaba ga dukan al’ummai na duniya.[3] Alkur'ani mai girma ya daukaka Annabi Ibrahim a matsayin abin koyi, mai biyayya ba mai bautar gumaka ba.[4]

A cikin wannan ma'ana, an kwatanta Annabi Ibrahim a matsayin wakiltar "mutum na farko a duniya ya mika wuya ga Haƙiƙanin Allahntaka kafin rarrabuwar ta zuwa addinan da suka rabu da juna ta hanyar bambance-bambancen tsari".[5] :18Musulmai sun yi imani da cewa Annabi Ibrahim da dansa Annabi Isma'il ne suka gina Ka'aba da ke garin Makka a matsayin gidan ibada na farko a duniya.

Ana gudanar da ranar Idin Al-Adha mai tsarki a Musulunci don tunawa da yadda Annabi Ibrahim ya sadaukar da dansa bisa umarnin Allah, da kuma karshen aikin hajji na Ka'aba.

Sadaukarwar Annabi Ibrahim

Musulmai sunyi imani cewa Annabi Ibrahim, wanda aka fi sani da Khalilullah (Larabci: خليل الله Trans: abokin Allah), ya zama shugaban salihai a zamaninsa kuma ta hanyarsa ne Adnaniyawa - Larabawa da Isra'ilawa suka zo. Ibrahim, a akidar Musulunci, ya bada gudummuwa kwarai da gaske wajen tsarkake duniya daga bautar gumaka a lokacin.

Annabi Ibrahim ya kawar da maguzanci a cikin ƙasashen Larabawa da mutanen Kan'ana. Ya tsarkake wurare biyu a ruhaniya tare da tsarkake gidajen ibada ta jiki. Annabi Ibrahim da Annabi Isma'il (Isma'il) sun kara kafa ayyukan hajji,[6] wanda har yanzu musulmai suke bi.

Musulmai sun yi iƙirarin cewa Annabi Ibrahim ya ƙara roƙi Allah ya albarkaci zuriyarsa, Annabi Isma'il da Annabi Is'haq (Ishak), kuma ya kiyaye zuriyarsa gaba ɗaya cikin tsarin Allah.

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 (Farhad ed.). Missing or empty |title= (help)
  2. [Al Kur'ani 87:19]
  3. [Al Kur'ani 2:124]
  4. [Al Kur'ani 16:120]
  5. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Glasse
  6. [Al Kur'ani 2:128]