Kasuwa
Kasuwa, wani keɓantaccen guri ne da ake tanada don haɗuwa a yi cinikayya wato saye da sayarwa. Gurin hada-hadar kasuwanci [1] Wanda ita kasuwa tana haɗa mutane daban-daban daga wurare mabam-banta da ƙasashe daban-daban kuma ita kasuwa kusan komai akwai a cikinta. Jam'in kasuwa shi ne kasuwanni haka kuma wanda yake harkar.



![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
market (en) ![]() |
Hashtag (mul) ![]() | Wochenmarkt da Market |



kasuwanci ana ce masa ɗan kasuwa. Ana yi wa kasuwa kirari da "kasuwa akai maki tilas in an ƙiya a kai maki babu" kasuwanni iri-iri ne akwai kasuwar dabbobi akwai kuma kasuwar hatsi da dai sauran kasuwanni. Akwai kasuwa da ake cinikayya ta cikin ƙasa akwai kuma ta ƙasa da ƙasa.[2]
Bunkasa Tattalin arziki
gyara sasheKasuwa dai baya ga bunkasa tattalin arzikin waɗanda ke yin kasuwancin, tana kuma bunkasa ko taimaka wa gwamnati ta hanyar samun kuɗaɗen shiga ta sigar biyan haraji daga `yan kasuwa. Akan bayar ko haraji a duk sati ko wata ko kuma ya danganta da yadda gwamnati ta tsara za ta rinka amsa a lokacin da ta tsara.