Mamman Bello Ali
Mamman Bello Ali (1958 – 26 Janairu 2009) shi ne Sanatan Najeriya mai wakiltar Yobe ta Kudu. Ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun jama'a daga shekarar 1999 zuwa 2007, sannan gwamnan jihar Yobe daga shekara ta 2007 har zuwa rasuwarsa a 2009. Har wayau ya kasance memba a jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
Mamman Bello Ali | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2007 - 27 ga Janairu, 2009 ← Bukar Ibrahim - Ibrahim Gaidam → District: Yobe South
3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 District: Yobe South
1999 - 2003 District: Yobe South | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Jimeta, 1958 | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Mutuwa | 27 ga Janairu, 2009 | ||||||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (sankaran bargo) | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna | ||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | All Nigeria Peoples Party |
Rayuwarsa
gyara sasheAn haifi Amman Ali a shekarar 1958 a Jimeta garin Adamawa, Najeriya. Mamman ya zauna ne a gidan mahaifinsa a garin Jimeta mafi rayuwarsa acan yayi, a wasu lokutan Yana tareda abokinsa Alhaji Mouktar Garba Ibrahim dan gidan Attah. Wa 'yannan sune wurare biyun da aka fi samun sa karfin wafatinsa. Mamman yayi wafati a ranar ashirin da shida na watan Janairu a shekarar 2009 lokacin da yake karban kulawan asibiti na cutar leukemia a ƙasar Florida.[1]
Asalin Ilimi
gyara sasheMamman Bello Ali yayi karatun firamare da ta sakandiri a garin Jimeta, yaje makarantan Numan craft dake garin Gongola Mamman yaje Kaduna Polytechnic domin kammala diplomarsa ta biyu wato Higher National Diploma (HND).[2] a shekara ta 1982, ya kuma karasa bautan ƙasa (NYSC) a nan garin Kaduna daga baya kuma ya fara aiki a Abuja, Nigeria.
Mutuwa
gyara sasheYana jinyar cutar sankarar bargo a wani asibitin Florida lokacin da ya rasu. [3]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ https://www.pointblanknews.com/Tributes/tribute4.html
- ↑ https://www.manpower.com.ng/people/15861/mamman-bello-ali
- ↑ Yobe State Governor, Mamman Bello Ali, 51, Dies in a Florida Hospital of Leukemia Archived 2018-09-20 at the Wayback Machine