Rukunin kamfanoni na Dangote ko Dangote Group kamfani ne na hadaka a Najeriya mallakin Alhaji[1] Aliko Dangote. Shi ne babban kamfani a yankin Afirka ta yamma kuma daya daga cikin manya a nahiyar Afirka. Kuma Kamfanin ya samar wa da mutane aikin yi a kalla sun kai dubu dari uku 300,000

Dangote Group

Bayanai
Suna a hukumance
Dangote Group
Iri kamfani
Masana'anta conglomerate (en) Fassara da cement industry (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Aiki
Harshen amfani Turanci
Kayayyaki
Mulki
Hedkwata Lagos,
Mamallaki Dangote Group
Tarihi
Ƙirƙira 1981
Wanda ya samar
dangote-group.com
Dangote da wasu mutane
Kamfanin dangote
Kamfanin fetur na Dangote
gidan aliko dangote

An samar da kamfanin ne a shekara ta alif Dari Tara da tamanin da daya 1981 da farko domin kasuwanci inda ya fara da shigo da sikari da siminti da shinkafa da kifi da sauran kayayyakin masarufi na bukatun yau da kullum don rarrabawa a kasuwannin Najeriya. Kamfanin ya cigaba ya zama babbban kamfanin da ke sarrafawa tare da samar da kayayyaki a shekara ta alif Dari tara da casssa,in da daya 1991, ya fara da sakar tufafi, sai kuma sarrafa fulawa, sai sarrafa gishiri, sai sarrafa sikiri. Daga nan kamfanin ya bunkasa zuwa samar da kamfanin sarrafa siminti. Kamfanin ya bunkasa zuwa sauran sassa na nahiyar Afrika.

[2]

A yanzu rukunin yana tafiyar da kamfanoni sama da goma sha,takwas 18 a kasahen Afrika guda goma. Babbar cibiyar rukunun kamfanonin Dangote tana jihar Lagos a Najeriya.

Tarihin kamfanin

gyara sashe

Aliko dangote ne ya kafa kamfanin bayan samun rance na dalar Amurika $3,000 daga hannun kawunsa. Ya fara ne da sayar da kayan abinci daga bisani kuma ya cigaba zuwa shigo da kayayyaki ta jirgin ruwa kamar siminti.

A yau kamfanin ya bunkasa sosai a Nahiyar Afrika. Kamfanin na samarwa tare da kasuwancin Shinkafa, Sikari, Fulawa, taliya, kayan ruwa, man fetur da iskar gas, samar da rukunun gidaje, harkar sadarwa, takin zamani da karafa.

Rarrabuwar Kamfani

gyara sashe

Kamfanin wanda ya shahara a huldar kasuwar duniya ta hada-hadar hannayen jari 'Stock Exchange' ya rarrabu zuwa kasashen Benin, Kamaru, Ghana, Najeriya, Afirka ta Kudu da Zambiya

Kamfanin sikari na Dangote shi ne babban kamfanin sikari a yankin Afrika makusantan Sahara.Cite error: Invalid <ref> tag; refs with no name must have content

  1. https://www.dangotecement.com/careers/
  2. https://www.dangoterefinery.org