Rukayya bint Muhammad

(an turo daga Ruqayyah)

Ruqayya bint Muhammad ( Larabci: رقية بنت محمدc. 601 zuwa Maris 624) ita ce babbar ‘yar Annabi Muhammadu da Khadija ta biyu. Ta auri khalifa na uku Uthman kuma ma'auratan sun haifi ɗa Abdallah. A shekara ta 624, Ruqayya ta rasu daga rashin lafiya.

Rukayya bint Muhammad
Rayuwa
Haihuwa Makkah, 598
Mutuwa Madinah, 14 ga Maris, 624
Makwanci Al-Baqi'
Ƴan uwa
Mahaifi Muhammad
Mahaifiya Khadija Yar Khuwailid
Abokiyar zama Sayyadina Usman dan Affan
Utbah ibn Abi Lahab
Yara
Ahali Ummu Kulthum, Zainab yar Muhammad, Abdullahi ɗan Muhammad, Yaran Annabi, Ibrahim ɗan Muhammad da Fatima
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Rayuwar farko

gyara sashe

An haife ta a Makka a shekara ta 601 ko 602 AD, Ruqayya ita ce ɗiya ta 3 kuma a mata itace ta biyu ga Muhammad da Khadija, matarsa ta farko, wadda ita ma ta kasance hamshakiyar 'yar kasuwa. [1] [2]

Rayuwar aure

gyara sashe

Auren ta da Utbah

gyara sashe

Tayi aure kafin watan Agusta, shekara ta 610 ga Utbah ibn Abi Lahab, amma ba a take auren ba. [3] Ruqayya ta musulunta lokacin da mahaifiyarta ta rasu. [4] [5] Lokacin da Muhammadu ya fara yin wa’azi a fili a shekara ta 613, kuraishawa sun tuna wa Muhammadu cewa sun “dauke masa kulawar ‘ya’yansa mata” kuma suka yanke shawarar mayar da su domin ya tallafa musu da kuɗin sa. Sai suka gaya wa Utbah cewa za su ba shi ‘yar Aban ibn Sa’id bn Al-As ko ‘yar Sa’id bn Al-As idan ya saki Ruqayya. [3] Bayan Muhammadu ya gargadi Abū Lahab cewa zai shiga wuta, Abu Lahab ya ce ba zai sake yin magana da ɗan sa ba har sai ya saki Ruqayya, wanda Utba ya yi hakan. [6] [7]

Auren ta da Uthman

gyara sashe

A shekara ta 615 Ruqayya ta auri wani fitaccen musulmi, Uthman ibn Affan. Ta yi masa rakiya a Hijira ta farko zuwa Abyssinia, [8] [9] [10] inda ta yi fama da zubewar ciki. Sun koma Abyssiniya a shekara ta 616, [11] [9] [10] kuma a nan Ruqayya ta haifi ɗa namiji Abd Allah a shekara ta 619. Abdallah ya rasu yana ɗan shekara shida a Madina. Ba ta da sauran 'ya'ya. [9] [10]

Uthman da Rukayya suna daga cikin waɗanda suka dawo Makka a shekara ta 619. [12] Uthman ya yi hijira zuwa Madina a shekara ta 622, kuma Ruqayya ta bi shi daga baya. [9] [10]

An ce Ruqayya tana da kyau sosai. Lokacin da aka aika Usama bn Zaid zuwa gidansu, sai ya tsinci kansa da kallonta ita da Uthman bi da bi. Muhammad ya tambayi Usama, shin ka taɓa ganin kyawawan ma'aurata fiye da waɗancan biyun? kuma ya yarda cewa bai taɓa ba. [13]

Ruqayya ta yi rashin lafiya a watan Maris shekara ta 624. Uthman ya samu uzuri daga aikin sojan sa domin ya kula da ita. Ta rasu a cikin watan, a ranar da Zaidu bn Haritha ya koma Madina da labarin nasarar da suka samu a yakin Badar . [14] [15] [10] Lokacin da Muhammadu ya koma Madina bayan yaƙin, danginta sun tafi kabarinta domin nuna alhinin su.

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. Muhammad ibn Ishaq. Sirat Rasul Allah. Translated by Guillaume, A. (1955). The Life of Muhammad, p. 83. Oxford: Oxford University Press.
  2. Muhammad ibn Saad. Kitab al-Tabaqat al-Kabir, vol. 8. Translated by Bewley, A. (1995). The Women of Madina, p. 10. London: Ta-Ha Publishers.
  3. 3.0 3.1 Ibn Ishaq/Guillaume p. 314.
  4. Ibn Saad/Bewley vol. 8 pp. 24-25.
  5. Muhammad ibn Jarir al-Tabari. Tarikh al-Rusul wa'l-Muluk. Translated by Landau-Tasseron, E. (1998). Volume 39: Biographies of the Prophet's Companions and Their Successors, pp. 161-162. Albany: State University of New York Press.
  6. Ibn Saad/Bewley pp. 24-25.
  7. Tabari/Landau-Tasseron pp. 161-162.
  8. Ibn Ishaq/Guillaume pp. 146, 314.
  9. 9.0 9.1 9.2 9.3 Ibn Saad/Bewley p. 25.
  10. 10.0 10.1 10.2 10.3 10.4 Tabari/Landau-Tasseron p. 162.
  11. Ibn Ishaq/Guillaume p. 146.
  12. Ibn Ishaq/Guillaume p. 168.
  13. Jalal al-Din al-Suyuti. Tarikh al-Khulafa. Translated by Jarrett, H. S. (1881). History of the Caliphs, p. 155. Calcutta: The Asiatic Society.
  14. Ibn Ishaq/Guillaume p. 328.
  15. Muhammad ibn Umar al-Waqidi. Kitab al-Maghazi. Translated by Faizer, R., Ismail, A., & Tayob, A. K. (2011). The Life of Muhammad, p. 51. Oxford & New York: Routledge.