Dauda Kahutu Rarara

Mawakin siyasa

Dauda Adamu Kahutu Rarara wanda aka fi sani da Rarara, an haife shine a ( jihar Katsina ) shahararren mawaƙin ƴan siyasa ne a Nijeriya, mawaƙi a fanin rera wakokin yan siyasa kuma marubucin waƙuqe, Ni Abdussamad nace Dauda Kahutu Rarara yafi kowa kudi a masana'antar Kannywood.[1] wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen rera waƙoƙin na yan jama,eyan(APC) All Progressive Congress a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2015, musamman ma ga shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari[2] da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari.[3].

Dauda Kahutu Rarara
Rayuwa
Sana'a

Rayuwar farko da ilimi Gyara

An haifeshi ne a jihar Katsina a wani kauye da ake kira Kahutu, Yayi karatun Alqur'ani a makarantar Almajiranci, wata hanyar gargajiya ce ta Hausawa ta koyon addinin Musulunci.wato (kolanta).

Siyasa Gyara

Rarara ya kasance sananne ne yayin babban zaben Najeriya na 2015, lokacin da yake rera wakoki da dama ga Muhammadu Buhari da kuma adawa da shugabancin Goodluck Jonathan a galibin wakokin nasa. A watan satumba na 2020, Rarara ya nemi gudummuwa daga masoyan Muhammadu Buhari, don tura masa Naira dubu daya domin sakin bidiyon minti biyu na yabon Muhammadu Buhari, cikin kasa da awanni 48 Ya karbi Naira miliyan 57 don sakin wakar wacce Ya yaba Muhammadu Buhari.

Wakokinsa Gyara

Dauda kahutu rarara yayi wakoki da dama, ga kaɗan daga cikin fitattun wakokinsa;

  • Masu Gudu-su-Gudu
  • Buhari ya Dawo
  • Baba Buhari dodar
  • Jahata ce
  • Kwana ɗarin Dallatu
  • Kano ta Gandujace
  • Ubban Abba zama daram

Shugaban 13x13 Gyara

Shine shugaban kungiyar matasan kannywood ta 13x13, wata kungiya ce ta adadin mutum sha ukku (13), kuma ko wanne mutum daya daga cikin su sha ukkun yana da mutum 13 dake karkashinsa.[4]

Sukar Gyara

Wasu futattun matasa sun afkawa Rarara yayin da yake daukar bidiyo a jihar Katsina. Ana zargin sa da wawure Naira Miliyan 100 da jam'iyyar siyasa ta All Progressive Congress ta ba wa duk wadanda ke rera wakoki ga ƙungiyar siyasa.[ana buƙatar hujja]

.

Manazarta Gyara