Aminu Bello Masari

Dan siyasan najeriya

Aminu Bello Masari About this soundAminu Bello Masari  (an haife shi ranar 29 ga watan Mayu, shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin (1950)).[1][2]

Aminu Bello Masari
gwamnan jihar Katsina

29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023
Ibrahim Shema
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

3 ga Yuni, 2003 - 6 ga Yuni, 2007
Ghali Umar Na'Abba - Patricia Etteh
District: Malumfashi/Kafur
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

1999 -
Rayuwa
Cikakken suna Aminu Bello Masari
Haihuwa Jahar Katsina, 29 Mayu 1950 (74 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulmi
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Hon. Aminu Bello Masari

Ya zama gwamnan jihar Katsina sakamakon samun nasara a zaɓen shekarar 2015, haka zalika kuma ya sake lashe zaɓen 2019 a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki. Ya riƙe muƙamin Kwamishinan ayyuka da muhalli da kuma sufuri na Jihar Katsina a tsakanin shekarar 1991 zuwa 1993. Gabanin zaman sa gwamna ya riƙe muƙamin kakakin Majalisar wakilai ta kasa. Shine gwanman jihar katsina har zuwa yau a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

 
Zargin sheman da samana da fadi da wasu kudade
 
Gwamna Aminu Bello Masari

Bayan da aka rantsar dashi a matsayin gwamna ba da daɗewa ba, sai Gwamna Masari ya bayyana cewa tsohon gwamnan da ya gabata watau Barista Ibrahim Shehu Shema ya ci kuɗaɗen da suka kai kimanin miliyan ɗari huɗu. Wannan turka-turka da wasu caje-caje da ke da nasaba da kuɗi su ka sa hukumar Economic and Financial Crimes Commission watau E.F.C.C ta gurfanar da Gwamna Shema a gaban kotu kan cajin almundahanar kuɗaɗen da suka kai kimanin biliyan goma sha ɗaya (N11 billion). [3] Hakazalika gwamnatin Masari ta kori zababbun shugabannin ƙananan hukumomi 34 da aka zaɓa a lokacin gwamnatin PDP. A nata ɓangaren jam'iyyar PDP ta reshen jihar Katsina, ta shigar da ƙarar gwamnatin jihar kan tunɓuke zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin.[4]

 
Aminu Bello Masari

[5]. On Saturday night was the day Masari to hand over to re-elect Governor,Governor Masari on his farewell talk thank the Katsina entire resident for giving him all the support during his eight year as Governor of the State, the ex-governor also asked for forgiveness for wrong he does during his year in office.

Farkon Rayuwa

gyara sashe

An haifi Aminu Bello Masari an haifeshi a ranar 29 ga watan Mayu, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin (1950).[6].

Aminu Bello Masari yayi matsayin speaker a majalisar dokoki ta ƙasa sannan shine gwamnan jihar Katsina tun 2015.[7]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Katsina decries call for Gov Masari's resignation". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 22 August 2021. Retrieved 22 February 2022.
  2. "Masari commends NYSC for promoting youth development and empowerment - The Nation Newspaper". thenationonlineng.net. Retrieved 3 March 2022.
  3. Francis Sardauna (31 May 2018). "Court Adjourns EFCC's Case Against Shema". AllAfrica. Retrieved 23 January 2020.
  4. Agency Report (September 4, 2018). "LG transition committees: Katsina PDP drags Masari to Supreme Court". Premium Times. Retrieved 23 January 2020.
  5. "Hotunan Ziyarar Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari A Muryar Amurka". VOA. Retrieved 23 Sat, 2019. Check date values in: |accessdate= (help)
  6. https://www.africa-confidential.com/profile/id/4131/Aminu_Masari
  7. https://www.africa-confidential.com/profile/id/4131/Aminu_Masari
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.