Ahmed Makarfi

Ɗan siyasan Najeriya

Ahmed Makarfi (An haife shi a ranar 8 ga watan Agusta,shekara ta alif dari tara da hamsin da shida 1956) a karamar hukumar Makarfi, jihar Kaduna. Ya kasance dan siyasa a Nijeriya, kuma tsohon gwamnar jihar Kaduna, da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya. Gwamnan jihar Kaduna ne daga shekara ta alif daritara da casa'in da tara ( 1999 ) zuwa shekara ta dubu biyu da bakwai ( 2007 ), bayan Umar Farouk Ahmed - kafin Namadi Sambo.[1] Kuma ya kasance membane na jam'iyyar PDP.[2][3][4][5]

Ahmed Makarfi
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

14 Nuwamba, 2011 - 6 ga Yuni, 2015 - Samaila Suleiman
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Kaduna North
gwamnan jihar Kaduna

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Umar Farouk Ahmed - Namadi Sambo
Rayuwa
Haihuwa Makarfi, 8 ga Augusta, 1956 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Tarihi gyara sashe

An haifi Ahmad Makarfi a ranar 8 ga watan Agustan shekara ta alif, 1956,a karamar hukumar Makarfi dake jihar Kaduna.

Siyasa gyara sashe

Ahmad Makarfi kwararren dan siyasa ne a Najeriya. Kuma cikakken dan jam’iyar PDP ne a Jihar Kaduna.[1]

Dangi da iyali gyara sashe

Matarsa ita ce Hajiya Asma’u Makarfi ta fara karatunta na firamari a shekara ta alif, 1977,a makarantar Kaduna Capital School, Inda ta fara samo ilimi akan harkan zamantakewa da dabi’a ta kula da yara.[6][7]

Rikicin PDP gyara sashe

A cikin shekara ta (2017), an cire Makarfi a matsayin Shugaban PDP kuma an ayyana Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban, amma bayan hukuncin mutum biyar na Kotun Apex, Makarfi ya dawo bakin aikinsa a matsayin Shugaban PDP na kasa.

A watan Yuni a shekara ta (2018), Makarfi ya bayyana cewa yana shiga cikin "gogaggun 'yan jam'iyya maza da mata" a fafatawar neman takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa a zaben shekara ta (2019). Ya ce adalci ne kawai ya shiga takarar bayan tattaunawa mai zurfi tare da jam’iyyarsa maza da mata da sauran masu ruwa da tsaki. Makarfi yana daya daga cikin 'yan takara (12) da sukayi takarar neman PDP a babban taron da akayi a Fatakwal a ranar (6) ga watan Nuwamba a shekara ta (2018). Daga cikin 'yan takara( 12 )da suka nemi tsayawa takarar,' yan takara hudu ciki har da shi kansa Makarfi sun fito ne daga jihohin Arewa maso Yamma. Aminu Tambuwal (Jihar Sakoto), Rabiu Kwankwaso (Jihar Kano), Attahiru Bafarawa (Jihar Sakoto) su ne sauran ‘yan takarar da suka kafa yankin. Manazarta sun yi hasashen cewa dimbin 'yan takara daga yankin zasu raba kuri'un wakilai daga yankin tsakanin masu fafatawa dakebada dama ga fitattun' yan takara daga wasu yankuna akan su. A zaben fidda gwani na PDP, Makarfi ya samu matsayi na (5) mai nisa bayan Atiku Abubakar wanda ya lashe zaben. Sakamakon rashin nasara daga firamare ya kawo karshen takarar shugaban kasa a shekara ta (2019). [8][9][10][11][12][13]

Bibiliyo gyara sashe

  • Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 https://www.africa-confidential.com/profile/id/2670/Ahmed_Makarfi
  2. "APC leaders behind Buhari's death rumor - Makarfi". Daily Post Nigeria. 2017-01-24. Retrieved 2017-07-12.
  3. Editor, Online (2017-07-05). "PDP: We'll Abide By Supreme Court Ruling, Says Sheriff". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2017-07-12.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  4. Editor, Online (2017-05-09). "Chibok Girls: Makarfi's PDP Comes Under Fire for Criticising Prisoner Swap". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2017-07-12.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  5. "2019: Who succeeds Ahmed? - The Nation Nigeria". The Nation Nigeria (in Turanci). 2017-07-03. Retrieved 2017-07-12.
  6. Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. p.p 160-161, ISBN 978-978-906-469-4.
  7. "Makarfi loses senatorial seat to CPC". Nigerian Daily. 29 April 2011. Archived from the original on 23 March 2012. Retrieved 3 May 2011.
  8. "Supreme Court declares Makarfi as authentic PDP Chair - The Nation Nigeria". The Nation Nigeria (in Turanci). 2017-07-12. Retrieved 2017-07-12.
  9. "PDP primary results: Atiku wins presidential candidacy". The Sun Nigeria (in Turanci). 2018-10-07. Retrieved 2020-04-08.
  10. "Atiku picks PDP presidential ticket in 'one-horse' race". TheCable (in Turanci). 2018-10-07. Retrieved 2020-04-08.
  11. Yusuf, Omotayo (2018-10-07). "Atiku to face Buhari in 2019 as former VP wins PDP presidential primary". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Archived from the original on 2019-12-21. Retrieved 2020-04-08.
  12. "Atiku Wins PDP Presidential Primary". SilverbirdTV (in Turanci). 2018-10-07. Archived from the original on 2021-06-22. Retrieved 2020-04-08.
  13. "PDP presidential primaries: How aspirants stand". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2018-10-07. Retrieved 2020-04-08.[permanent dead link]