Zaynab Alkali
Zaynab Alƙali (An haife ta a shekara ta 1950) ta kasance farfesa ce a harshen Turanci. Kuma ta fito ne daga gidan Turah-Mazila dake jihar Borno da jihar Adamawa.[1]
Zaynab Alkali | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jihar Borno, 1950 (73/74 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Hausawa |
Harshen uwa | Hausa |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Bayero Bachelor of Arts (en) |
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci |
Muhimman ayyuka | The still born (en) |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Kuruciya da Karatu
gyara sasheAn haifi Zainab Alkali ne a garin Tura-Mazila a jahar Borno dake Arewacin ƙasar Najeriya a shekarar ta 1950 ,Ta fara karatun ta na sakandire a Queen Elizabeth dake jiharar Illor. Sannan ta tafi zuwa Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ta samu digirin ta na farko dana biyu. Daga baya ta koma Jami'ar Bayero dake jihar Kano shekarar a 1973 inda ta karanta turanci har ta kai ga ta samu digiri na uku wato matakin Dakta.[2]
Zainab Alkali ta shahara a rubuce-rubucen taƙaitattun ƙagaggun labarai, littafinta na farko data wallafa ya shahara, shi ne littafinta 'The Stillborn' a shekara ta 1984, sannan sai littafinta na biyu 'Virtuous woman' wadda Longman suka wallafa a shekara ta 1987, Zainab Alkali dai ta kasance marubuciya kuma ta wallafa littafai da dama, kuma littattafanta sun kasance an fassara su zuwa yaruka daban-daban kamar Jamusanci, larabci, Faransanci, Safaniyanci da dai sauran su. Tana daga cikin mata marubuta na farko a Arewacin Najeriya.
Rayuwarta
gyara sasheZainab ta auri tsohon shugaban jami'ar Maiduguri Mohammed Nur Alkali kuma suna da 'ya'ya shida tare.[3]
Ayyukan ta
gyara sasheLittattafan ta
gyara sashe- The Stillborn, Lagos: Longman (Drumbeats), 1984, ISBN 978-0-582-78600-4
- The Virtuous Woman, Longman Nigeria, 1987, ISBN 978-978-139-589-5
- Cobwebs & Other Stories, Lagos: Malthouse Press, 1997, ISBN 978-978-0230296.
- The Descendants, Tamaza, 2005, ISBN 978-978-2104-73-1
- The Initiates, 2007, ISBN 978-978-029-767-1.
Wanda ta gyara
gyara sashe- Zaynab Alkali, Al Imfeld (eds), Vultures in the Air: Voices from Northern Nigeria, Ibadan-Kaduna-Lagos: Spectrum Books, 1995, ISBN 978-978-2462-60-2
Girmamawa
gyara sasheNassi
gyara sashe- Kabir, Hajara Muhammad,. Mai talfawa matan arewicin. [Nijeriya]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Kabir, Hajara Muhammad ([2010-]). Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
- ↑ Margaret Busby, Daughters of Africa, London: Cape, 1992, p. 782.
- ↑ Galleria, Nigeria. "Nigeria Personality Profile". Nigeria Galleria. Galleria Media Limited. Retrieved 11 March 2019.