Yahaya Abdulkarim
Yahaya Abdulkarim (an haife shi a ranar 21 ga watan Agusta, shekara ta alif ɗari tara da arba'in da hudu 1944), ɗan siyasar Najeriya ne wanda yayi gwamnan jihar Sokoto, tsakanin watan Janairun shekara ta alif dari tara da casa'in da biyu 1992, zuwa watan Nuwamban shekara ta alif dari tara da casa'in da uku 1993, a lokacin ƙoƙarin Janar Ibrahim Babangida zuwa mulkin demokraɗiyya.[1] Bayan komawar dimokuraɗiyya a shekara ta alif 1999, ya zama mai mulki a jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara, kuma ya yi aiki na wani lokaci a majalisar ministocin shugaba ƙasa Olusegun Obasanjo.[2]
Yahaya Abdulkarim | |||||
---|---|---|---|---|---|
ga Maris, 2006 - 29 Mayu 2007 ← Adeseye Ogunlewe
ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993 ← Bashir Salihi Magashi - Yakubu Mu'azu → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Talata-Mafara, 21 ga Augusta, 1944 (80 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Farkon aiki
gyara sasheAn kuma haifi Yahaya Abdulkarim a ranar 21 ga watan Agustan shekarar 1944 a garin kwatarkwashi dake jihar Zamfara.[3] Mahaifinsa jami'in Hukumar Mulki ne.[4] Ya shiga aikin farar hula na Jihar Arewa maso Yamma a matsayin malami, kuma ya riƙe muƙamai daban-daban kafin ya yi ritaya a shekarar 1989 a matsayin Darakta-Janar a Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare Tattalin Arziƙi ta Jihar Sakkwato.[3]
Gwamnan Jahar Sokoto
gyara sasheAn kuma zaɓi Abdulkarim a matsayin gwamnan jihar Sokoto, Najeriya a watan Janairun shekara ta alif 1992, mai wakiltar National Republican Convention (NRC). A watan Nuwamban shekara ta 1993, gwamnatin mulkin soja ta Janar Sani Abacha ta tilasta masa sauka daga muƙaminsa.[1] A lokacin da ya ke riƙe da muƙamin, ya samu saɓani da Attahiru Bafarawa, shugaban jam'iyyar NRC a jihar. Rikicin ya ci gaba, kuma a lokacin da Bafarawa ya zama Gwamnan Jihar Sakkwato a shekarar 1999. ya bi manufar yin watsi da duk wata hanya da gine-gine da gwamnatin Abdulkarim ta gina.[5] A shekarar 1992, Abdulkarim ya rattaɓa hannu a kan ƙudirin kafa Makarantar Kimiyya ta Talata Mafara, daga baya aka canza mata suna Abdu Gusau Polytechnic.[6]
Daga baya aiki
gyara sasheA watan Satumbar shekarar 2002, an naɗa Abdulkarim a wani ƙaramin kwamiti na Hukumar Raya Yankin Neja-Delta don sa ido kan ayyukan raya ƙasa na biliyoyin Naira da aka ƙaddamar a jihohi tara da ake haƙo mai.[7]
An kuma naɗa Abdulkarim ƙaramin ministan ayyuka a majalisar ministocin shugaba Olusegun Obasanjo a watan Yulin shekarar 2005.[8] Ya maye gurbin Alhaji Saleh Shehu a wannan matsayi.[9] A cikin watan Nuwamba shekarya ta 2006, ya buɗe tsare-tsare don faɗaɗa shirye-shiryen dawo da hanyoyin tituna don ƙaddamar da lokacin Kirsimeti.[10] Lokacin da aka kori Ministan Ayyuka, Adeseye Ogunlewe, a cikin watan Maris, shekara ta 2006, an ƙara masa girma zuwa Ministan Ayyuka.[ana buƙatar hujja] kasance a gaban majalisar dattijai don binciken halinsa yayin da yake wannan ofishin.[11]
Ya kuma kasance ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara a jam’iyyar PDP wanda bai yi nasara ba a zaɓen watan Afrilun shekarar 2007.[12] A shekarar 2007, jam'iyyar PDP ta jihar Zamfara ta rabu gida biyu, ɗaya ƙarƙashin jagorancin Abdulkarim, ɗaya kuma ƙarƙashin jagorancin tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Aliyu Gusau. A watan Maris na shekarar 2008, Abdulkarim ya jagoranci wata tawaga daga Zamfara inda ya nemi shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Prince Vincent Ogbulafor, da ya hana Gusau tsoma baki cikin harkokin jam’iyyar.[2]
A watan Oktoban shekarar 2008, an ba da rahoton cewa yana neman muƙamin minista a majalisar ministocin shugaba Umaru Ƴar'Adua.[13]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 https://www.worldstatesmen.org/Nigeria_federal_states.htm
- ↑ 2.0 2.1 http://allafrica.com/stories/200803280677.html
- ↑ 3.0 3.1 http://allafrica.com/stories/200911110210.html?page=2
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-03-30. Retrieved 2023-03-14.
- ↑ https://thenationonlineng.net/web2/articles/30856/1/Bafarawa-Traits-from-his-past/Page1.html
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-12-14. Retrieved 2023-03-14.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2012-03-04. Retrieved 2023-03-14.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2012-01-11. Retrieved 2023-03-14.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-03. Retrieved 2023-03-14.
- ↑ http://allafrica.com/stories/200512020140.html
- ↑ https://guardian.ng/sunday_magazine/article10/indexn3_html?pdate=251009&ptitle=Bad%20Roads:%20Shameful%20Faces%20Of%20A%20Nation&cpdate=291009[permanent dead link]
- ↑ https://www.hugedomains.com/domain_profile.cfm?d=triumphnewspapers.com
- ↑ http://allafrica.com/stories/200810310744.html