WACTIPSOM
Gamayyar Haɗin Kan Yammacin Afirka Ta Yaki Da Fataucin Bil Adama da Baƙi (Turanci:West African Coalition Against Trafficking in Persons and Smuggling of Migrants WACTIPSOM), hukuma ce mai rajin daƙike fataucin Bil Adama da Baƙi a yankin Yammacin Afirka. Bisa da yin la'akari da ƙaruwar samun matsala ta fataucin Bil Adama a ƙasashen yankin Yammacin Afirka ne ƙasashen sukayi gamayyar samar hukumar ta WACTIPSOM.[1]
Tarihi
gyara sasheAnyi taron ƙaddamar da hukumar ne a ranar 17 ga Nuwamba, 2021 a otal din Nicon Luxury Abuja kuma taron ya samu halartar wakilai daga ƙasashen yammacin Afirka 14 (Benin, Burkina Faso, Cape Verde, Gambia, Ghana, Guinea, Gini, Ivory Coast, Liberia, Mali, Nijar, Najeriya, Senegal, Saliyo, da Togo); da wakilan MDAs, Tarayyar Turai, da Ofishin Jakadancin Diflomasiya.
Hukumar tana samun goyon bayan hukumomi irin ta na ƙasa da ƙasa kamar hukumar Matakin yaki da safarar mutane da safarar bakin haure a Najeriya A-TIPSOM, Gidauniyar Ibero-America don Gudanarwa da Manufofin Jama'a (FIIAPP) sai kuma Cibiyar sadarwa ta CSOs mai ƙalubalantar Fataucin Bil Adama, Gallazawa da kuma Aiyukan Azabtarwa (NACTAL).[2][3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://atipsom.com/2021/12/09/launching-of-west-african-coalition-against-trafficking-in-persons-and-smuggling-of-migrants-wactipsom/
- ↑ https://atipsom.com/2021/06/04/pre-launch-briefing-of-west-african-coalition-against-trafficking-in-persons-and-smuggling-of-migrants-wactipsom/
- ↑ https://thecitizenng.com/nigerian-ambassador-to-mali-raises-alarm-over-modern-slavery/