Alhusain ɗan Ali

Jikan Annabi Muhammad (saw)Dan Aliyu bin Abi Dalib Dan Fatimah bintu Muhammad
(an turo daga Uosaine dan Ali)

Hussain Ibn Ali Bin Abutalib jikan manzon Allah ne, Allah ya yarda dashi, Dan Nana Fatima diyar manzan allah (SAW), uwargidan Aliyu dan Abutalib, dan'uwansa shi ne Alhasan dan Ali dan Abutalib. Hussain shine wanda yan 'Shi'a ke darajawa a matsayin daya daga cikin Imamansu na farko.[1]

Alhusain ɗan Ali
3. Imam of Twelver Shiism (en) Fassara

669 - 680
Alhasan dan Ali - Ali ibn Husayn
Rayuwa
Haihuwa Madinah, 9 ga Janairu, 626
ƙasa Khulafa'hur-Rashidun
Khalifancin Umayyawa
Harshen uwa Ingantaccen larabci
Mutuwa Karbala, 12 Oktoba 680
Makwanci Imam Husayn Mausoleum (en) Fassara
Yanayin mutuwa death in battle (en) Fassara (killed in action (en) Fassara)
Killed by Shemr (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Sayyadina Aliyu
Mahaifiya Fatima
Abokiyar zama Layla bint Abi Murrah al-Thaqafi (en) Fassara
Umm Ishaq bint Talhah (en) Fassara
Shahrbanu (en) Fassara
Rubab bint Imra al-Qais (en) Fassara
Yara
Ahali Ummu Kulthum bint Ali, Sayyida Ruqayya bint Ali, Zaynab bint Ali (en) Fassara, Alhasan dan Ali, Hilal ibn Ali (en) Fassara, Jafar ibn Ali (en) Fassara, Abbas ibn Ali (en) Fassara, Muhsin ibn Ali (en) Fassara, Abdullah ibn Ali ibn Abi Talib (en) Fassara, Ubaidillah bin Ali (en) Fassara, Muhammad ibn al-Hanafiyyah (en) Fassara, Abu Bakr ibn Ali (en) Fassara, Umar ibn Alí (en) Fassara, Uthman ibn Ali da Fatima bint Ali (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Harsuna Ingantaccen larabci
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a Shugaban soji, Malamin akida da maiwaƙe
Aikin soja
Ya faɗaci Battle of the Camel (en) Fassara
Yakin Siffin
Battle of Nahrawan (en) Fassara
Yaƙin Karbala
Imani
Addini Musulunci
Husayn Masjid an-Nabawi Calligraphy
Portraits of the Imāms Ḥasan (d. 670), Ḥusayn (d. 680), Shāfi`ī (d. 820) and Abū Ḥanīfa (d. 767), with `Abbāsid revolutionary Abū Muslim (d. 755)

Matsayinsa

gyara sashe

A ranar uku ga watan Sha'aban mai albarka na shekara ta huɗu bayan hijira aka yi wa Manzon Allah (S.A.W) albishir da haihuwar Hussaini (A.S.). Don haka sai ya gaggauta tafiya gidan Ali da Zahara (A.S), ya ce wa Asma'u bin Umais: "Asma'u kawo min ɗana." Sai Asma'u ta kawo wa Manzo shi ɗauke a farin zani. Sai Manzo ya yi murna da ganinsa, ya rungume shi, sannan ya kira sallah a kunnensa na dama, ya kuma yi ikama a na hagu, sannan ya dora shi a cinyarsa sai aka ga yana kuka. Sai Asma'u, cikin mamaki, ta tambaye shi, cewa: "Wa kakewa kuka?" Sai Manzo (s.a.w.a) yace: "Dan nan nawa." Sai Asma'u ta ce: "Yanzun nan aka haife shi." Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce:

"Ya Asma'u!, wata azzalumar kungiya karkatacciya ce za ta kashe shi a bayana, Allah ba Zai hada su da cetona ba".

Sannan sai ya ce:

"Ya Asma'u! Kar ki faɗa wa Fatima wannan labari, domin ba ta daɗe da haihuwarsa ba (1)".

Sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya sami sako daga Allah Madaukakin Sarki, game da sunan abin haihuwarsa mai daraja; sai ya waiwayi Ali (a.s.) ya ce: "Ka sa masa suna Hussaini".

Matsayin Imam Husaini (a.s)

gyara sashe

Hakika Abu Abdullahi al-Husain (a.s.) na da babban matsayi. Bayan ayoyin Alkur'ani da suka ambaci matsayinsa cikin matsayin Ahlulbaiti (a.s.), wadanda muka ambata a baya, kamar su Ayar Tsarkakewa, Ayar Mubahala, Ayar Kauna da sauransu; akwai hadisan Annabi masu yawa da ke nuna girman matsayinsa da daukakar darajarsa. Daga cikin su akwai:

1- Abin da ya zo cikin Sahih al-Tirmizi cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Husaini daga gare ni yake, ni kuma daga gare shi nake. Allah Ya so wanda ya so Husaini. Husaini jika ne daga cikin jikoki(2). [2]

2- An ruwaito daga Salman al-Farisi, ya ce: na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: "Hasan da Husaini 'ya'yana ne, wanda ya so su ya so ni, wanda kuma ya so ni Allah zai so shi, wanda kuwa Allah Ya so zai shigar da shi Aljanna. Kuma wanda ya fusata su ya fusata ni, wanda kuma ya fusata ni Allah zai yi fushi da shi, wanda kuwa Allah Ya yi fushi da shi zai shigar da shi wuta(3)".

3- An ruwaito daga Ali bin Husaini daga babansa, daga kakansa (a.s.), cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya kama hannun Hasan da Husaini (a.s.) sannan ya ce: "Wanda ya so ni ya kuma so wadannan biyun da babansu da mamansu, zai kasance tare da ni ranar kiyama(4)".

Dabi'un Imam Husaini (a.s)

gyara sashe

Hakika kasantuwan Imam Hasan (a.s) ya tashi ne karkashin kulawar kakansa Manzo (s.a.w.a), babansa Ali da mahaifiyarsa al-Zahara (a.s.), ta sa dabi'unsa na misalta sakon Allah Madaukaki a tunance, aikace da halayya. A nan za mu bayar da wasu 'yan misalai.

1- Shu'aib bin Abdul-Rahman ya ruwaito cewa: "An ga wani tabo a bayan Imam Husaini (a.s.) a Karbala; sai aka tambayi Imam Zainul-Abidin (a.s) game da shi, sai ya amsa da cewa: "Wannan ya samo asali ne daga buhunan abinci da yake dauka a bayansa yana kai wa gidajen matan da mazansu suka mutu da marayu da miskinai".

2- Ya taba bi ta wajen wasu miskinai alhali suna cin abinci a akushi, sai suka yi masa tayi, sai ya sauka ya ce: "Lallai Allah ba Ya son masu girman kai", sai ya ci abincin. Sai ya ce musu: "Na amsa muku, to ni ma ku amsa min." Sai suka amsa, suka tafi tare da shi har zuwa gidansa, sai ya ce wa matarsa: "Fito da duk abin da kika adana (5)".

3- An taba ce masa: Me ka fi tsoro daga Ubangi-jinka? Sai ya ce: "Babu mai amintuwa daga ranar kiyama sai wanda ya ji tsoron Allah a duniya".

4- A daren goma ga watan Muharram Imam Husaini (a.s.) ya bukaci rundunar Umayyawa 'yan adawa, da su jinkirta masa wannan daren yana mai cewa: "Don muna so mu yi salla ga Ubangijinmu da daddare mu kuma nemi gafarar Sa, domin Shi ya san ni ina son yin sallah gare Shi da tilawar Littafin Sa da yawan addu'a da istigfari".

1- Dabarasi, cikin A'alamul-Wara Bi A'alamil-Hudah, shafi na 218; da Khawarizmi, cikin Maktalul-Husaini, juzu'i na 1, shafi na 87.

2- Fadha'ilul-Khamsah, juzu'i na 3, shafi na 262-263.

3- A'alam al-Warah, shafi na 219.

4- Sibd Ibn al-Jauzi, cikin Tazkiratu Khawas al-Ummah, babin da ya yi magana a kan 'Son Manzon Allah da Hasan da Husaini'.

5- Abu Ilm, cikin Ahlulbait, babin dake magana a kan tawali'un Imam Husaini da gudun duniyarsa.


Manazarta

gyara sashe