Ezenwo Wike

Dan Siyasa a Najeria
(an turo daga NYESOM WIKE)

Ezenwo Nyesom Wike CON, (An haife shi a ranar sha uku 13 ga watan Disamba shekara ta alif ɗari tara da sittin da bakwai 1967),[1] an sansa da sunaye daban-daban, kamar Ezebunwo Nyesom Wike, Nyesom Ezenwo Wike, Nyesom Ezebunwo Wike ko Nyesom Wike Dan Nijeriya, Dan siyasa kuma lauya wanda shine Gwamnan Jihar Rivers na shida kuma maici a yanzu.[2] Shi mutumin Ikwerre ne daga Rumuepirikom a Obio-Akpor, Jihar Rivers. Dan jam'iyar People's Democratic Party (PDP) kuma yayi Karatun a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Rivers.

Ezenwo Wike
gwamnan jihar Rivers

29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023
Rotimi Amaechi
Rayuwa
Cikakken suna Ezenwo Nyesom Wike
Haihuwa 24 ga Augusta, 1967 (57 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Eberechi Wike
Karatu
Makaranta Jami'ar jihar Riba s
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Lauya
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
hoton enze wike
wike a taro


An naɗa Wike a matsayin Ministan Ilimi karami a ranar 14 July 2011. Wike ya zama Ministan Ilimi na wucin gadi, bayan Mrs Ruqayyatu Rufa'i an kore ta, amma ya ijiye mukamin domin zuwa yin kamfen ɗin sa na neman Gwamnan Jihar Rivers. Inda Viola Onwuliri yamaye gurbinsa.[3] A shekara ta dubu biyu da sha huɗu (2014), ya samu nasarar tsayawa takarar jihar sa ta Rivers a karkashin jamiyar People's Democratic Party (PDP) yazabi tsohon Sakataren Gwamnatin jihar wato Ipalibo Banigo a matsayin mataimakin sa.

 
Ezenwo Wike a gefe

Wike ya doke Dakuku Peterside na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Tonye Princewill na Jam'iyar Labour Party (LP) a zaben Gwamnonin Nijeriya na ranar 11 ga watan Afrilu, shekarar 2015, inda ya zama zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Rivers.[4][5][6][7]

A watan Maris na shekarar dubu biyu da ashirin da biyu (2022), Wike ya bayyana cewa zai tsaya takarar kujerar shugaban Najeriya a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) gabanin babban zaben 2023, Atiku Abubakar ne ya doke shi da ƙuri'u ɗari uku da saba'in da ɗaya (371), yayin da Wike ya samu ƙuri'u ɗari biyu da talatin da bakwai (237) a matsayin wanda ya zo na biyu a yayin zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) wanda aka gudanar a babban filin wasa na ƙasa MKO ABIOLA, Abuja a ranakun ashirin da takwas (28) da kuma ashirin da tara (29) ga Mayu, shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu (2022).

 
Ezenwo Wike

Shugaba Bola Tinubu ya nada Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja a ranar 16 ga watan Agustan 2023[8], bayan tantancewa da amincewar da majalisar dattawa ta yi akan cewa ya dace a bashi[9].

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.google.com/amp/s/www.vanguardngr.com/2023/10/the-rise-and-rise-of-nyesom-wike-by-donu-kogbara/amp/
  2. "Perceptions 2023: Nyesom Wike, Yahaya Bello". THISDAYLIVE (in Turanci). 2022-02-05. Retrieved 2022-03-11.
  3. Cabinet reshuffle: Onwuliri now Minister of Education (State), 22 October 2014, Retrieved 10 February 2016
  4. "Archived copy". Archived from the original on 2015-04-02. Retrieved 2015-04-13. Unknown parameter |deadurl= ignored (|url-status= suggested) (help)CS1 maint: archived copy as title (link)
  5. "What's New in 1.5?". Archived from the original on 25 October 2014. Retrieved 22 December 2014. Cite has empty unknown parameter: |publishereducation.gov.ng= (help)
  6. "AS WIKE FACES THE JURY". THEWILL. Archived from the original on 24 August 2013. Retrieved 22 December 2014.
  7. "Students Enterprise of Nigeria " Chief Ezenwo Wike". Gecng.vom. Archived from the original on 25 October 2014. Retrieved 22 December 2014.
  8. https://www.vanguardngr.com/2023/08/breaking-tinubu-appoints-wike-minister-of-fct-umahi-minister-of-works/
  9. https://punchng.com/just-in-national-assembly-clears-wike-for-ministerial-role/