Ipalibo Banigo
Ipalibo Gogo Banigo (née Harry; an haife ta ranar 20 ga watan Disamba shekara ta 1952) likita ce ƴar Najeriya, kuma ƴar siyasa itace mace ta farko mataimakiyar gwamnan jihar Ribas.[1] Ƴar jam’iyyar PDP (People’s Democratic Party), ta riƙe mukamai daban-daban a ma’aikatar lafiya ta jihar Ribas. A lokacin da take hidimarsa jihar ta, ta riƙe muƙamin Daraktar Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Jama’a, Kwamishina mai riƙon ƙwarya, Darakta-Janar da Sakatare taa din-din-din a jihar. Ta fara yin fice a shekarar 1995, a matsayin sakatariyar gwamnatin jihar Ribas kafin ta zama shugabar ma'aikata ta jihar. A watan Disambar shekarar 2014, Ezenwo Wike ya zaɓe ta a matsayin abokiyar takararsa a zaɓen shekara ta 2015. An zaɓe ta mataimakiyar gwamna kuma ta karɓi muƙamin a ranar 29 ga watan Mayu shekarar 2015.
Ipalibo Banigo | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
13 ga Yuni, 2023 - District: Rivers West
29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023 ← Tele Ikuru
5 Oktoba 1995 - 5 ga Yuli, 1999 | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Degema, 20 Disamba 1952 (71 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
Jami'ar Harvard University of London (en) Harvard T.H. Chan School of Public Health (en) | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da Doctor of Medicine (en) | ||||||
Employers | UNICEF | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | Rivers State People's Democratic Party (en) |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Banigo a ranar 20 ga watan Disamba 1952 ga ahalin Harry na Obuama a Degema, Jihar Rivers. Lokacin da take matashiya, ta sami takardar shedar makarantar Afirka ta Yamma (Division One) da kuma takardar shaidar sakandare a Kwalejin Queens, Legas. Ta samu kyaututtuka saboda kwazonta a fannin Chemistry, Biology da Adabin Turanci (Literature). A shekarar 1968, ta lashe kyautar BBC ta waƙar ɗalibai. Kafin ta kammala makarantar sakandare, ta kasance babbar dalibar da ta fi kowane ɗalibi a cikin shekarun karatun ta daga 1969 zuwa 1970 ƙwazo a kowane fanni. Ta samu digiri na farko a fannin likitanci, tayi digirin-digirgir a Kwalejin aikin asibiti a Jami’ar Ibadan, sannan ta halarci Makarantar Kiwon Lafiyar Jama’a ta Jami’ar Harvard. digirinta na biyu ya kasance tsakanin 1990 zuwa 1992, Banigo ta sami difloma a fannin Lafiyar fata daga Jami'ar London.
Aiki
gyara sasheBanigo ta fara aikinta ne a ma’aikatar lafiya ta tashar ruwa ta Jihar Ribas, inda ta yi aiki a matsayin mai yin rajista kuma mai ɗaukar rajistar masu haihuwa da kuma babbar jami’ar lafiya. Haka ta zamo mai ba da shawara ga likitan fata a Jami'ar Fatakwal, bayan ta zama shugabar Makarantar Fasaha ta Lafiya ta Jihar Ribas a shekara ta 1985. A lokacin da take a Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Ribas, ta rike ofisoshi guda biyar da suka haɗa da Daraktan Ma'aikatar Kiwon Lafiyar Jama'a, Mukaddashiyar Kwamishinan, Darakta-Janar, kuma Babbar Sakatariya. A ranar 5 ga Oktoba 1995 aka naɗa Banigo a matsayin Sakatariyar Gwamnatin Jihar Ribas, ta ci gaba da aiki har zuwa 5 ga Yuli 1999. Ta kuma yi aiki na tsawon watanni biyar, daga watan Mayu 1998, a matsayin Shugabar Ma'aikatan Jihar Ribas. Yayin da ta yi ritaya, Banigo ta ci gaba da ba da gudunmawa ta a jihar inda daga baya aka naɗa ta mai ba da shawara kan harkokin kiwon lafiyar jama’a na kamfanin Shell Petroleum Development Company Nigeria. Bugu da ƙari, ta rike ofisoshin Babban Darakta da Sakatare a Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta ƙasa. Wasu daga cikin mambobinta sun haɗa da Majalisar Gudanarwa ta Jami'ar Calabar, Hukumar Gudanarwa ta Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Najeriya, haka ta riƙe kwamitin Abinci Jihar Ribas, tayi aiki da hukumar Kula da Asibitin Jihar Ribas da Hukumar Bincike ta DFID. An kuma naɗa ta shugabar ayyuka na UNFPA, UNICEF da shugabar kwamitin agaji na jihar Ribas. A cikin Disamba 2014, an zaɓe ta don zama mataimakiyar dan takarar gwamna Ezenwo Wike a zaben 2015. Da ita dashi Dukkan su ƴan jam’iyyar PDP kuma an zaɓe su, sun karɓs ragamar mulki a ranar 29 ga Mayu 2015. A halin yanzu Banigo ita ce mataimakiyar gwamnan jihar Ribas ta 6 kuma mace ta farko. A ranar 29 ga Afrilu, 2021, ta kasance daga cikin masu ba da shawara kan harkokin kiwon lafiya da suka halarci wani taron da St Racheal's Pharmaceuticals Nigeria ta shirya don tunawa da ranar zazzaɓin cizon sauro ta duniya na 2021 da aka gudanar a Legas, inda ta gabatar da wasu dabaru kan yadda za'a shawo kan matsalar zazzaɓin cizon sauro har sai ya koma Zero-Malaria a Najeriya nan da shekaru 10 masu zuwa. A ranar 20 ga Satumba, 2020, ta zama shugabar kwamitin mutane bakwai da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ƙaddamar don ƙaddamar da wasu cibiyoyin kiwon lafiya a jihar.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Godwin, Ann (2018-03-31). "Wike, Deputy, Obuah preach forgiveness, love, friendship". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in English). Archived from the original on 2022-02-23. Retrieved 2022-03-06.CS1 maint: unrecognized language (link)