Muammar Mohammed Abu Minyar Gaddafi Lafazi; (/ˈmoʊəmɑːr ɡəˈdɑːfi/;. Ya rayu daga shekara ta 1942 zuwa ashirin ga watan Oktoba shekara ta 2011), Muammar al-Gaddafi da larabci: معمر محمد أبو منيار القذافي. Amfi saninsa da Konel Gaddafi ko Gaddafi, Yakasance dan gwagwarmayar kasar Libya ne, Dan siyasa, kuma mai taimakon mutanensa. Ya mulki Kasar Libiya matsayin sa na jagoran juyin mulkin da ta samar da Jamhoriyar Larabawa ta Libya wato Libyan Arab Republic da turanci, tun daga shekara ta 1969 har zuwa 1977, sannan aka canja sunan jagorancinsa zuwa Shugaba Dan'uwa wato "Brotherly Leader" na babban jam'iyar talakawa, da akafi sanida Great Socialist People's Libyan Arab Jamahiriya tun daga shekara ta 1977 har zuwa shekaran 2011. Gaddafi yakasance dan rajin cigaban larabawa ne amma daga baya ana ganin ya watsar da hakan ya fara bin ra'ayin Kansa. Gaddafi ya rike mukamai da dama aciki da wajen kasarsa, daga ciki ya rike Shugaban kungiyar kasashen Afirika wato African Union (AU) daga biyu ga watan Fabrairu a shekara ta 2009 har zuwa talatin da daya ga watan Janairu. Gaddafi yayi karatunsa a Jami'ar Kasar Libya da kuma Jami'ar Soji ta Benghazi, Gaddafi musulmi ne, mai bin ahlus-Sunnah, wato sunni Islam.

Simpleicons Interface user-outline.svg Muammar Gaddafi
Moamer el Gadafi (cropped).jpg
Chairperson of the African Union (en) Fassara

2 ga Faburairu, 2009 - 31 ga Janairu, 2010
Jakaya Mrisho Kikwete (en) Fassara - Bingu wa Mutharika (en) Fassara
Prime Minister of Libya (en) Fassara

16 ga Janairu, 1970 - 16 ga Yuli, 1972
Mahmud Sulayman al-Maghribi (en) Fassara - Abdessalam Jalloud (en) Fassara
Brotherly Leader and Guide of the Revolution (en) Fassara

1 Satumba 1969 - 23 ga Augusta, 2011
← no value - no value →
Rayuwa
Cikakken suna مُعمّر محمد أبو منيار القذّافي
Haihuwa Qasr Abu Hadi (en) Fassara, 7 ga Yuni, 1942
ƙasa Libya
Ƙabila Qadhadhfa (en) Fassara
Mutuwa Sirte (en) Fassara, 20 Oktoba 2011
Makwanci Libyan Desert (en) Fassara
Yanayin mutuwa kisan kai (ballistic trauma (en) Fassara
lynching (en) Fassara)
Killed by National Transitional Council (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Mohammed Abdus-Salam
Mahaifiya Aisha Ben Niran
Abokiyar zama Fethiye Nuri al-Khaled (en) Fassara  (1969 -  1970)
Safia Farkash (en) Fassara  (10 Satumba 1970 -  2011)
Yara
Karatu
Makaranta Benghazi Military University Academy (en) Fassara
Joint Services Command and Staff College (en) Fassara
University of Libya (en) Fassara
Fu Hsing Kang College, National Defense University (en) Fassara
Matakin karatu Doctor of Sciences (en) Fassara
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, marubuci da hafsa
Tsayi 185 cm
Muhimman ayyuka The Green Book (en) Fassara
Third International Theory (en) Fassara
Kyaututtuka
Fafutuka Pan-Arabism (en) Fassara
anticolonialism (en) Fassara
Arab nationalism (en) Fassara
Third International Theory (en) Fassara
Aikin soja
Fannin soja Libyan Army (en) Fassara
Armed Forces of the Libyan Arab Jamahiriya (en) Fassara
Digiri colonel (en) Fassara
Ya faɗaci First Libyan Civil War (en) Fassara
Libyan–Egyptian War (en) Fassara
Uganda–Tanzania War (en) Fassara
Chadian–Libyan war (en) Fassara
First Liberian Civil War (en) Fassara
Toyota War (en) Fassara
Second Congo War (en) Fassara
Battle of Tripoli (en) Fassara
Ethiopian Civil War (en) Fassara
1969 Libyan coup d'état (en) Fassara
Imani
Addini Ƙur'aniyya
Mabiya Sunnah
Jam'iyar siyasa Libyan Arab Socialist Union (en) Fassara
Arab Socialist Union (en) Fassara
IMDb nm0300490
Muammar al-Gaddafi Signature.svg

TarihinsaGyara

An haife Gaddafi a kusa da garin Sirte daga gidan talakawa makiyayan Larabawa, Gaddafi mai matukar kishin Larabawa ne tun yana makaranta a Sabha, daga nan ya shiga Royal Military Academy, Benghazi. Yana cikin soja ne yahada kungiyar data kifar da mulkin turawan yamma a kasar Wanda suke amfani da sarkin kasar na wancan lokacin wato Senussi Mulkin Idris a shekarar 1969. Daga amsar mulki, Gaddafi ya sauya Libiya daga mulkin sarauta zuwa jamhoriya inda yan gwagwarmayarsa ke mulki da umurninsa. Daga nanne ya kora dukkani Italiyawa da turawan dake da sansani a kasar zuwa kasashen su, kuma ya karfafa dangantakarsa da sauran kasashen Larabawa, musamman da Shugaba Gamal Abdel Nasser's na kasar Misra (Egypt) tare da Neman hadin kan kasashen Afirika. Gaddafi ya kafa Shari'a a matsayin abun gudanar da dokokin kasar, tare da daukan tsarin jagoranci musulunci. Ya mayar da arzikin man fetur din kasar mallakar gwamnati kuma ya rika amfani da kudaden domin karfafa sojojin kasar, da taimakawa kasashen wake, da taimakawa mutane wurin ginin gidaje, kiwon lafiya, ilimi da sauransu.

Gaddafi ya sauya fasalin Kasar Libya zuwa mulkin daya Kira "Jamahiriya" wato Kasar Al'ummah da turanci ("state of the masses") a shekarar 1977. A shekara ta 1970s zuwa 1980s, yakin iyaka tsakanin Libya da kasashen Misra da Cadi da taimakon yan tawayen kasashen waje, da zargin da ake masa na daukan nauyin Lockerbie bombing a kasar Scotland yasa kasar tazama saniyar ware a duniya.

ManazartaGyara