Kunama jam'in ta shine (kunamu) Fulani suna kiranta da Yaare, kunama ɗaya ce daga cikin ƙwari masu cizo ko kuma harbi ta hanyar cakawa abin cizo ƙari. Haka kuma tana daga dabbobi waɗanda sam ba'a kiwon su amma tana zama a gida musamman gidajen ƙauye, kunama tanada haɗarin gaske don saboda idan ta harbi mutum tana daɗewa tana ma mutum zugi wato takan daɗe bata faɗi ba. Wani lokacin ma har tsawon kwanaki uku (3) zata kai tana yima mutum zugi da raɗaɗi da zafi. [1][2]

Kunama
Scientific classification
KingdomAnimalia
SubkingdomBilateria (en) Bilateria
PhylumArthropoda
ClassArachnida (en) Arachnida
order (en) Fassara Scorpiones
Koch, 1837
General information
Tsatso scorpion as food (en) Fassara
kunama
Kunamu
Kunama
kunama
kunama
dayigiram ɗin kunama
farar kunama
kunama
ajiyayayyar kunama
kunama
Kunama
kunama da diyarta
kunama

.

Bayanin Kunama

gyara sashe

Kunama kala-kala ce akwai baƙa ƙirin wannan ita tafi ko wace kunama girma akwai kuma baƙa-baƙa, akwai mai ruwan ƙasa sai kuma wadda take kamar fara kuma ba fara ba. Kunama tanada wutsiya da ƙambori guda biyu a kanta waɗanda take amfani dasu wajen miƙo wani abu kamar abincinta da kuma ƙwari. Wutsiyar kunama dashi take harbin duk wani abinda ya matse ta ko mutum ko dabba a wutsiya/bindin kunama akwai wani tsini wanda yafi allura tsini da wannan harbi a lokacin da tayi ɗanawa Mutun ko dabba wannan tsini wani Ruwan dafi ne take ɗigawa cikin jikin abinda ta ciza to wannan ruwan shine zai dinga yin raɗaɗi da zafi har sai ya sallace. Kuma tana amfani da ƙarinta wajen kare kanta daga harin waɗansu dabbobi.

 
baƙar Kunama cikin ganyaye
 
ƙarin kunama
 
kunama
 
kunama
 
kunama da maciji

Rayuwar Kunama

gyara sashe
 
kala Kalan kunama

Kunama tana rayuwa ne wajajen Sahara duk da cewa ana samun kunama a kowane yanki na Duniya sai yankin Antaktika (Antarctica) ne kawai ba'a samun ta. Jinsin kunama ya kai 2,500 kunama takan ci ƙwari (insects) ne don ta rayu irin su fara, buzuzu, zanzaro gara da dai sauransu, sai dai masu bincike sun gano kunama tana cin ciyawa, duk da itama kanta kunamar kalacin (abincin) waɗansu dabbobin ne kamar ƙadangare, maciji da sauransu. Wani abin mamaki shine kunama tana amfani da waɗannan ƙamborin ta biyu a lokacin saduwa tsakanin miji da mace don ƙarin nishaɗi. Kunama tana haihuwa ne ta hanyar yin ƙwai sai daga baya ta ƙyanƙyashe ƙwansu matane masu kula da ƴaƴansu, ance kunama takan goya ƴaƴan ta a bayanta. A cikin Nau'ikan kunama 2,500 guda 25 ne kawai idan suka ciza mutum zai iya mutuwa.

Manazarta

gyara sashe
  1. Zane, Damian (5 November 2020). "'Na yi matuƙar farin ciki da aka sanya wa kunama sunana'". bbc hausa. Retrieved 17 August 2021.
  2. "Kunamu sun harba mutum 450 a Masar, uku sun mutu". BBC Hausa.Com. 13 November 2021. Retrieved 14 November 2021.