Ƙadangare jam'in shi shi ne ƙadangaru, mace kuma ana ce mata ƙadangaruwa.[1] yana daga cikin dabbobi masu tafiya da ƙafa huɗu a wani bincike kuma ana cewa yana daga dabbobi masu rarrafe. Kuma kusan ko'ina a faɗin duniya ana samun shi, sai dai kaɗan daga cikin wasu yankuna irinsu, Antaktika da Island. Ƙadangare da mage. Ƙadangaru suna nan nau'i daban-daban wato kala-kala akwai ja, baƙi mai ratsin fari, yalo da dai sauran kaloli. Haka kuma, Nau'ukan ƙadangaru (species) ya kai dubu shida (6,000). [2]

Ƙadangare
organisms known by a particular common name (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Reptilia (en) Fassara
ƙadangare akan dutse/jangwalegwada
Ƙadangare da mage
Kadangare
kadan gare

Ƙadangaru suna faɗa da junansu musamman maza daga cikinsu kuma mafi akasari suna faɗan ne saboda mata.

Hoton jangwalegwada
wannan wani baƙin ƙadangare ne

Ƙadangaru suna cin ƙwari ne a matsayin abincinsu amma wani lokacin suna cin abincin da mutane suke ci kamar tuwo, wake da sauransu. Mafi akasarin ƙadangaru ƙanana ne girman su madaidaici ne, kamar tsaka Ko da yake tsaka tana cikin jinsin ƙadangaru. Mafi yawan ƙadangaru ƙwai suke yi don haihuwa, sukan yi ƙwai kusan ɗari. Haka kuma Hausawa na yin wata karin magana wai "ƙadangaren bakin tulu a ƙyale shi ya ɓata ruwa a kashe shi a fasa tulu" ma'anar wannan karin magana shi ne (wato kamar idan wani mutum ya matsa wa wani, kuma shi bai da ikon rabuwa da wanda ya matsa mashi ɗin), shi kenan wannan mutumin ya zame ma shi ƙadangaren bakin tulu.[3] Ƙadangare mafi girma a duniya shi ne Komodo dragon. [4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "sunan ƙadangare". hausadictionary.com. 11 March 2019. Retrieved 15 September 2021.
  2. "THE REPTILE DATABASE". reptile-database.org. 10 November 1995. Retrieved 9 July 2021.
  3. "Kenya : Matar da ta zamewa masu aikata laifi a Kenya ƙadangaren bakin tulu". BBC Hausa. 25 January 2021. Retrieved 9 July 2021.
  4. "Komodo dragons". bbc news. 25 January 1956. Retrieved 9 July 2021.