Ƙuli-ƙuli
Ƙuli-ƙuli (Groundnut cake) Kalmar ƙuli-ƙuli dai kalma ce da take a cikin harshen hausa. Haka zalika ƙuli-ƙuli ana iya cinsa ta hanyoyi da dama wasu sukan sanya shi a cikin gari su sha, wasu kuma sukan iya cinsa da Bazan-ƙwaila, wasu kuma suna cin sa haka nan zallansa.[1] Abinci ne na mutanen yammacin Afrika wanda ake samar dashi daga gyada. Sanannen abinci ne a ƙasashen Najeriya, Benin, Arewacin Kamaru da Ghana. Ana iya cin sa shi kadai. Ana kuma cin shi da koko, fura, kamu, kuma wani lokacin ana yin kwado da shi. Kuma ana haɗa shi wajen yin Tsire da Kilishi.[1][2].
Ƙuli-ƙuli | |
---|---|
Kayan haɗi | Gyaɗa |
Kayan haɗi | Gyaɗa, seasoning (en) , chili pepper (en) , sukari da gishiri |
Tarihi | |
Asali | Najeriya |
Yadda ake haɗa Ƙuli-ƙuli
gyara sasheDa farko ana samun Gyaɗa bayan an bare ta sai a soya ta sannan a murje ta a fece wato a hure dukan bawon gyadar. Daganan kuma sai a markada ta. Bayan an markada tane kuma za'ayi amfani da Turmi ayi ta juya ta ana juyata har sai manta duka an gama matse shi, ita kuma gyadar ta koma Tunkuza. Wannan tunkuzar za'a dauka a sarrafa ta zuwa irin yadda ake bukatar ta kamar gutsure-gutsure ko a tabe. Daganan sai dora Man gyadar da aka matse daga tunkuzar a kasko sai a hura wuta, idan man yadau zafi sosai sai a rinka zuba curi-curi ko tababbiyar tunkuzar cikin man ana soyawa anayi ana dan juyawa kadan kadan. Bayan ya gama soyuwa to shikenan Ƙuli-ƙuli ya kammalu.[3]
Hotuna
gyara sashe-
Gyaɗa da ake sarrafawa ayi Kuli-Kuli
-
Wata mai soya Kuli-Kuli
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-11-30. Retrieved 2020-12-27.
- ↑ https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
- ↑ Ibrahim, Salisu (21 November 2021). "Mu leka madafa: Dalla-dalla yadda ake hada wani nau'in Kuli-Kuli mai ban sha'awa". Legit.hausa.ng. Retrieved 22 November 2021.