Turmi wani abu ne daga cikin ka yan aikin gida wanda aka sassaƙa shi domin a dinmga daka da shi, ana sassaƙa shi daga itace masu karfi. Turmi ya kasu kashi biyu, Turmin da aka sassaƙa da Turmin ƙarfe, Turmin da aka sassaƙa shi ne Wanda ake aikin gida da shi, kamar daka da jajjagen kayan miya da dai sauran su. shi kuma Turmin karfe shi ne Turmin da ake daka magani a cikin sa ko kuma Turare, kamar kwalli, sabulu da sauransu.

Turmi
dyad (en) Fassara da product category (en) Fassara
Bayanai
Amfani comminution (en) Fassara
Kayan haɗi ceramic (en) Fassara, karfe, katako da bedrock (en) Fassara
Wooden_mortar_and_pestle_from_the_Philippines
Turmi
turmi
Grinding pigment
wani tsohon turmi da ake jima dashi

Ana kuma amfani da turmi wajen daka, kamar irin su dakan Fura irin Fulani haka, har ma da dakan tuwo wani lokacin. Ana kuma dakan magani da shi, ana yin jajjagen kayan miya misali ba sai an kai markade ba, ana kuma dakan ƙasar gini da dai sauran su. Kusan kowane gida akwai turmi saboda amfanin turmi koda amarya za'a kai sai an kuma haɗa ta da turmi (sai an siya mata turmi). Turmi shine Tilo Turame kuma shine jam'i.[1]

Shi Kuma Turmi baya yiwwuwa ayi amfani dashi dole saida Taɓarya itama Taɓarya sassaƙa ta akeyi kamar yadda ake sassaƙa Turmi. Akan ma mutum lakabi da turmi sha daka idan ya shahara sosai. [2]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://hausadictionary.com/turmi
  2. "Sana'ar sussuka". rumbunilimi.com.ng. Archived from the original on 18 April 2021. Retrieved 20 September 2021.