Kilishi
wanda aka fi sani da naman shanu na Najeriya, yana daya daga cikin kayan marmarin naman da ake samu ko na naman shanu, da naman laushi ko na chevon, kuma ya zama ruwan dare a tsakanin Hausawa a Arewacin Najeriya
Kilishi naman kilishi na daya daga cikin abincin da malam bahaushe ke ji da shi. Kilishi abu ne mai dadyi kwarai da gaske. Ko da yake malam bahaushe ne aka fi sani da cin naman kilishi. sannan da yawan al’umman ƙasar Najeriya sun fada wa son cin naman Kilishi, musamman ga Matasan kasar gaba daya. kilishi dai bushashshen nama ne, ana samun shi a Najeriya, Nijar, Kamaru da kuma Cadi. Ana hada shi da barkono, Kuli-kuli, albasa kuma da gishiri. Kilishi nama ne ake reɗe shi yayi falenfalan mara kauri sannan ya haɗe shi da Kuli-kuli, sa'annan a Gasa shi.[1][2]
Kilishi | |
---|---|
Kayan haɗi | naman shanu, cayenne pepper (en) , gishiri da albasa |
Tarihi | |
Asali | Nijar da Najeriya |
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54203041
- ↑ https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html