Gyaɗa
Gyaɗa (peanut) wani abinci[1] ne, asalinsa tsiro ne da ake shukawa, yana kuma fitar da ƴaƴa a cikin kasa ƙarƙashin jijiyoyinta. Kuma ana sarrafa shi ne don amfani da shi a matsayin abinci da sauransu ta hanyoyi daban-daban kamar wurin yin kunu[2], mai.[3][4] (mangyada), Madara[5], kuli kuli, ko zubawa a miyar taushe, da sauransu. Ana iya dafa gyada[6] ana iya soyata, ana kuma yin kantu. Gyada[7] na da sinadarin dake gina jiki, "protein" wanda ke da amfani sosai a jiki, musamman ma wajen kara girman jiki da bai wa jiki kariya, shiyasa yake da kyau a riƙa amfani da shi a cikin abinci. Kuma ita gyada ta kasu Kashi daban daban, akwai, Kampala, yar dakkar, Mai bargo da sauransu.[4]
Gyaɗa | |
---|---|
oil seed (en) ![]() ![]() ![]() ![]() | |
![]() | |
Tarihi | |
Mai tsarawa | Gyaɗa |






In da ake nomawa
gyara sasheYawancin inda suke nomata. Zamfara da Nasarawa da Kaduna da kuma Kwara. Duk dadai yanzu akwai sabon irin gyada da yake yi a jihohin yankin gabashin kasar nan, musamman ma jihohin Enugu da Anambra.[8]
Hanyoyin Sarrafa Gyada
gyara sasheAna Sarrafa gyada ta hanyoyi daban-daban kuma ana amfani da ita a duk fadin duniya, sai dai a nan za mu duba kadan ne daga irin hanyoyin da ake sarrafa gyada a matsayin abinci.
- Madaran Gyada, za a iya yin madara da gyada, idan aka sami danyen gyada sai a bare ta, a wanke sannan kuma a bari ta jiku a ruwa, sai a niketa, idan aka nika sai a tace, bayan an tace sai a dafa, idan ya dahu sai a bar ta ta huce, shikenan an samu madarar gyada, za a iya bai wa yara wadanda ba su samun cikakken abinci domin karin lafiya.
- Mangyada, za a iya hada mai da gyada idan aka samu gyada aka bare ta, aka bar ta ta bushe, ko kuma aka samu wanda aka riga aka busar, sai a soya ta ba da wuta sosai ba ko kuma za a iya kin soyawa, soyawa ba dole ba ne, idan an soya, sai a nika ta, to, ta zama tunkuza bayan an nika, daga nan sai a matse tunkuzar ta hanyar juyawa, za'a ga mai din na kadan kadan daga jikin tunkuzar.
ana sarrafa gyada a samar da man kuli kuli
Gyadar da aka sarrafa
gyara sashe-
Taben kuli, ana cin shi da koko
-
Loliyayyen kuli da aka sarrafa shi da gyadar
-
soyayyar gyada
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.premiumtimesng.com/2024/06/shirin-samar-da-abinci-gwamnan-kano-zai-sayo-wa-manoman-kano-takin-zamani-na-naira-biliyan-5/&ved=2ahUKEwjh9vOjiveGAxUeSEEAHcyACwYQxfQBKAB6BAgPEAI&usg=AOvVaw33ahKAHlMMMWmYGM6UrmJc
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailytrust.com/cholera-fg-asks-nigerians-to-avoid-locally-prepared-kunu-zobo/&ved=2ahUKEwjV9eO7iveGAxUIZ0EAHR79Cb0QxfQBKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw0RHiougysLpROT0LScucDs
- ↑ https://www.voahausa.com/a/cin-kwayaoyi-dangin-su-gyada-bashi-da-matsala-ga-mata--ga-mata-masu-ciki/1831526.html
- ↑ 4.0 4.1 https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-ƙasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/labarai-53648022.amp&ved=2ahUKEwiO55nriveGAxVkW0EAHfrjCt8QyM8BKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw35Q7RRfrfA4uWo1iVNfewv
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.leadership.ng/uwargidan-gwamnan-kebbi-ta-tallafawa-mata-500-da-buhunan-gyada-da-tsabar-kudi/&ved=2ahUKEwiVwab_iveGAxVQSEEAHcQGBGIQxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw29zgtRSKX1HtpA6G1F-IIc
- ↑ https://proveg.com/ng/recipes/kunnu-gyada/
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/sarrafa-albarkatun-gona-gyada-3/