Jeremiah Useni

dan siyasar Najeriya

 

Jeremiah Useni
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
John Nanzip Shagaya - Nora Daduut
District: Plateau South
ma'aikatar Babban birnin tarayya

1993 - 1998
Muhammad Gado Nasko - Mamman Kontagora
Governor of Bendel State (en) Fassara

ga Janairu, 1984 - ga Augusta, 1985
Samuel Ogbemudia - John Mark Inienger (en) Fassara
Rayuwa
Cikakken suna Jeremiah Timbut Useni
Haihuwa Langtang, Nijeriya, 16 ga Faburairu, 1943 (81 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Karatu
Makaranta Makarantar Sojan Najeriya
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da civil servant (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party

Jeremiah Timbut Useni (an haife shi a ranar 16 ga Fabrairu 1943) Laftanar- Janar na sojan Najeriya mai ritaya ne, ya taba rike mukamin minista mai kula da babban birnin tarayya Abuja a karkashin mulkin soja na Sani Abacha . Ya yi wa Najeriya hidima ya rike mukamai daban-daban kamar Ministan Sufuri da Kwata-Master Janar na Sojojin Najeriya. ya kuma taba zama mataimakin shugaban daya daga cikin manyan jam'iyyu a Najeriya, jam'iyyar All Nigeria Peoples Party . An zabe shi Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta Kudu a jihar Filato, Najeriya a zaben kasa na watan Maris 2015 . Useni ya yi takara ne a dandalin jam'iyyar People's Democratic Party (PDP).[1]

Aikin soja gyara sashe

Useni ya yi fice ne a Najeriya lokacin da aka nada shi Gwamnan Soja a Rubutacciyar Jihar Bendel ta Najeriya a watan Janairun 1984. A 1998, Useni a lokacin ministan babban birnin tarayya Abuja, an yi ta yayatawa a matsayin magajin Janar Sani Abacha . Useni ya bayyana cewa, an yanke shawarar nada Abdulsalami Abubakar ne bisa ka’ida. Bayan shekaru goma, Useni yasha fadar cewa Abacha ya mutune a matsayin mutuwa dag allah, sabanin jita-jitar da ake yadawa cewa ya mutu ne bayan ya ci tuffa mai guba.[2]

Da yake magana a watan Afrilun 2008, Ministan Babban Birnin Tarayya, Aliyu Modibbo Umar, ya dora alhakin matsalolin da babban tsarin Abuja ke da shi a kan gwamnatin Useni a matsayin minista a gwamnatin mulkin soja ta Abacha.

Siyasa gyara sashe

A cikin watan Agustan 2001, an nada shi shugaban wata tawaga daga kungiyar tuntuba ta Arewa domin ganawa tare da tattaunawa akan muradu yanki da gwamnonin jihohin Arewa dan sauran shugabanni. A shekarar 2003, ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar ANPP na kasa ta Arewa. A cikin Nuwamba 2004, an sakashi shi a cikin gwagwarmaya na cikin gida na ANPP tare da Cif Donald Etiebet, Shugaban jam'iyya ne Kasa.

A watan Mayun 2006, ya bar ANPP ya zama shugaban sabuwar jam'iyyar, Democratic People's Party, tare da wasu mambobin jam'iyyar ANPP. Duk da haka, an dakatar da shi har abada a cikin Disamba 2008, saboda ya ce mutuwar Ken Saro-Wiwa sadaukarwa ce ta kasa. Biodun Ogunbiyi ne ya gaje shi, wanda ya soki rashin shugabancin Useni, wanda ya haifar da gaza samun kujeru a majalisar dattawa ko ta wakilai a zaben Afrilun 2007. Useni ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a watan Afrilun 2011 a jam'iyyar DPP, amma Victor Lar na PDP ya doke shi. Daga baya ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Filato ta kudu a shekarar 2015 a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party wanda ya lashe zaben.

Gwamna gyara sashe

A watan Oktoban 2018, Jeremiah Useni ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar a PDP domin ya tsaya takarar gwamnan jihar Filato a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party. Ya sha kaye a babban zaben da aka yi a hannun Simon Lalong wanda ya samu kuri'u 595,582 zuwa Useni na 546, 813. Useni ya kalubalanci zaben Simon Lalong a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Filato kan cewa Lalong bai cancanci ya zama Gwamna ba, bayan da ya mika wata takardar shaida ta daban ga hukumar zabe (INEC) mai dauke da suna daban da na Gwamna mai ci yanzu. na Jihar Filato, Simon Bako Lalong.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a Halima Salami ta yi fatali da karar Useni da ke tabbatar da zaben Lalong saboda rashin kwararan hujjojin da ke tabbatar da saɓanin sunaye a cikin takardar shaidar Lalong da ya miƙa wa INEC. Useni ya daukaka kara kan hukuncin kotun daukaka kara da kotun koli amma ya sha kaye. Hukuncin da kotuna ta yanke ya kawo karshen burinsa na yin mulki a jihar Filato a 2019.

Manazarta gyara sashe

Template:AbujaFCTMinisters