Langtang, Nijeriya

Gari a Jihar Plateau, Najeriya

Langtang birni ne, kuma ƙaramar hukuma ce a Jihar Filato, Nijeriya. Garin yana a yankin kudancin jihar Filato kuma ya haɗe da; Tunkus, Shendam, Kanam da Wase ta hanyar titi.

Langtang, Nijeriya

Wuri
Map
 9°08′30″N 9°47′28″E / 9.14164°N 9.79101°E / 9.14164; 9.79101
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Yana da sakatariyar karamar hukuma da fadar Ponzhi Tarok dake tsakiyar garin. Gida ne ga Manyan Janar-Janar na Sojojin Najeriya, waɗanda suka hada da Janar Domkat Bali (marigayi), Joseph Nanven Garba (marigayi), Jeremiah Useni, Joshua Dogonyaro (marigayi), John Shagaya, Jonathan Temlong, Musa Gambo, Yakubu Rimdam, da Ishaku Pennap.. Sauran sun hada da Air Marshal Jonah Wuyep, Air Vice Marshal Napoleon B. Bali, Janar Samuel Nankpak Abashe, Air Commodore Bernard Banfa da kuma Janar Muhammad A. Najib. Gari ne ga dattawan jihohi; Cif Solomon Lar (Gwamnan farar hula na farko a jihar Filato) (marigayi), Cif Ezekiel S. Yusuf (marigayi) (shugaban zartarwa na farko na karamar hukumar Langtang) da Reverend Canon Selchang Miner.

Ilimi da Kiwon Lafiya

gyara sashe

Garin Langtang yana da Babban Asibiti da makarantu da suka bazu ko'ina cikin ƙaramar hukumar waɗanda suka haɗa da Kwalejin Mata na Gwamnatin Tarayya, Langtang, Makarantar Sakandaren Gwamnati Langtang. Har-wayau garin na da madatsun ruwa guda biyu da kuma matatar ruwa da don jama'ar garin.

Babbar ƙabilar garin ita ce Tarok, harshensu shine Tarok, kuma manyan addinan su shine Kiristanci da ATR. Suna samar da amfanin gona kamar gyada, gero, masarar Guinea da sauransu.[1]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "Plateau State". Nigeria Direct. Federal Ministry of Information and National Orientation. Archived from the original on 2007-04-18. Retrieved 2007-04-21.