Nora Daduut

yar siyasar Najeriya

Nora Ladi Daduut [lower-alpha 1] (an haife ta a ranar 10 ga watan Mayun shekarar 1953) Farfesa ce kuma ƴar siyasa a Najeriya.[1][2] Ita ce Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu Sanata a Majalisar Dokokin Najeriya ta 9.[3] Jami'ar Jos ta ɗauke ta zuwa matsayin farfesa a cikin shekarar 2018.[4] Ita ce mace ta farko a majalisar dattawa daga jihar Filato.

Nora Daduut
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi mace
Ƙasar asali Najeriya
Suna Nora
Shekarun haihuwa 10 Mayu 1953 da 1953
Wurin haihuwa Filato
Harsuna Turanci
Sana'a ɗan siyasa, Farfesa da Malami
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ilimi a Jami'ar Jos
Ɗan bangaren siyasa All Progressives Congress
Mamba na Sanatocin Najeriya na Majalisar Dokoki ta Kasa ta 9
Personal pronoun (en) Fassara L484

Sana'a gyara sashe

Daduut farfesa ce a Faransanci kuma ta yi murabus daga matsayin shugaban sashen Faransanci a Jami'ar Jos ta Jihar Filato.[5]

Sana'ar siyasa gyara sashe

A zaɓen Sanatan Plateau ta Kudu na shekarar 2020, ta wakilci jam’iyyar All Progressives Congress a zaɓen inda ta samu ƙuri’u 83,151, yayin da babban abokin hamayyarta a zaɓen Hon. George Daika, mai wakiltar jam'iyyar PDP, ya samu ƙuri'u 70,838.[6] An rantsar da ita a majalisar dattawa a ranar 15 ga watan Disamban shekarar 2020.[7]

Bayanan kula gyara sashe

  1. Also spelled Dadu'ut.

Manazarta gyara sashe