Ibrahim Saminu Turaki
Alhaji Ibrahim Saminu Turaki (An haifeshi ranar 14 ga watan Yuni, 1963). attajiri ne kuma dan siyasa, tsohon gwamna kuma tsohon sanata. Shi ne gwamnan Jahar Jigawa na shida, sannan kuma gwamnan farar hula na biyu.[1]
Ibrahim Saminu Turaki | |||||
---|---|---|---|---|---|
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 District: Jigawa North-West
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 ← Abubakar Maimalari - Sule Lamiɗo → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Birnin Kazaure, 14 ga Yuli, 1963 (61 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Hausawa | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Haihuwa
gyara sasheAn haife shi a ranar 14 ga watan Yuni shekara ta 1963 a garin Kazaure.[2]
Karatu
gyara sasheA Kudu Central Primary School ya yi karatunsa na Firamare, daga nan kuma sai ya wuce zuwa kwalejin gwamnatin tarayya ta Kaduna (Federal Government College, Kaduna), daga nan sai makarantar share fagen shiga jami'a ta Zariya, sai kuma ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya (Ahmadu Bello University, Zaria), inda ya samu Digiri.[3]
Siyasa
gyara sasheGwamnan Jihar Jigawa
gyara sasheAn zabe shi gwamnan Jihar Jigawa a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999 a karkashin tutar jama'iyyar ANPP (All Nigerian People's Party).[4]
Gudunmawar da ya Bada
gyara sasheYa bada gagarumar gudunmawa wajen habbaka wannan jaha ta Jigawa a kowane fanni tare kuma da bada fifiko wajen habbaka tattalin Arzikin jahar a hukumance da kuma daidaikun jama'a.[5] Samar da makarantar koyon kimiyyar kwamfuta mai suna 'Informatics Institute' da ke Kazaure wacce take ita ce ta farko a Najeriya da kuma cibiyar bayar da sabis din Intanet ta garin Dutse mai suna 'Galaxy ITT' na daga cikin manyan nasarorin da ya samu.[6]
Barinsa Mulki
gyara sasheYa bar wannan kujera ta shugabancin Jahar Jigawa a shekarar 2007 bayan da aka gudanar da zabe sannan kuma ya damkaa kujerar mulkin jahar a hannun Alhaji Sule Lamido , shi kuma ya wuce zuwa zauren majalisar dattawa ta tarayyar Najeriya a matsayin sanata mai wakiltar Jigawa ta Area.[7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ibrahim Saminu Turaki". National Assembly of Nigeria. Archived from the original on 3 March 2016. Retrieved 4 October 2009.
- ↑ Ibrahim Saminu Turaki's Weird Kites". ChatAfrik. 1 June 2008. Archived from the original on 24 October 2008. Retrieved 4 October 2009.
- ↑ Nigeria Politics & Security" (PDF). Menas. 29 December 2006. Archived from the original (PDF) on 3 October 2011. Retrieved 4 October 2009.
- ↑ TURAKI WANTED THE WORLD TO KNOW JIGAWA". Nigeriaworld. 24 July 2007. Retrieved 4 October 2009.
- ↑ Senator Turaki Faces Legal Action in Niger Republic - Over 86 Housing Units". Daily Trust. 16 November 2008. Retrieved 4 October 2009.
- ↑ Adamu Amadu (18 May 2011). "Lamido/Turaki: From politics to court" . Nigerian Tribune . Archived from the original on 29 March 2012. Retrieved 17 June 2011.
- ↑ Lamido: Great expectations, many problems". The Source Magazine. 18 June 2007. Archived from the original on 7 January 2009. Retrieved 4 October 2009.