Datti Abubakar
Datti Sadiq Abubakar ya kasance gwamnan soja na jihar Anambra a Najeriya daga Yuli 1978 zuwa Oktoba 1979 a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo.[1]
Datti Abubakar | |||
---|---|---|---|
ga Yuli, 1978 - Oktoba 1979 ← John Kpera - Jim Ifeanyichukwu Nwobodo → | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Datti Sadiq Abubakar | ||
Haihuwa | jahar Kano, 30 ga Maris, 1939 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Hausawa | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Mutuwa | 25 ga Faburairu, 2005 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheYa yi karatu a Kwalejin Rumfa, Kano.[2] A watan Yulin shekarar 1966 Laftanar Datti Abubakar, mai suna Recce, ya kasance a kurkukun Abeokuta lokacin da aka kashe yawancin jami'an Igbo, sun taka rawar gani a juyin mulkin da suka hambarar da Manjo-Janar Johnson Aguiyi-Ironsi.[3]
Ayyuka
gyara sasheGwamna
gyara sasheAn naɗa Abubakar gwamnan soja na jihar Anambra a watan Yulin 1978, ya rike wannan mukamin har zuwa watan Oktoba 1979.[1] Ya sanya makarantun a ƙarƙashin ikonsa ta hanyar kwamiti na dubawa tare da manyan iko akan manufofi da ma'aikata.[4] Bayan manyan rikice-rikice na addinai a jihar Kano a 1980, ya kasance memba a Kotun Binciken Rukunin Kano don bincika dalilai da bayar da shawarwari. kum ya kasance musulmi mazauin garin Kano.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-01-04.
- ↑ Musa Umar Kazaure (June 18, 2003). "Rumfa college Kano: School under royal eyes". Daily Trust. Archived from the original on 2012-03-04. Retrieved 2010-01-04.
- ↑ Nowa Omoigui. "Operation Aure (2): Planning to Overthrow General Ironsi". Gamji. Retrieved 2010-01-04.
- ↑ "Staff Discipline in the Anambra State Education Commission: A Review of Nsukka Education Zone from 1980 - 1988". University of Nigeria. September 1990. Retrieved 2010-01-04.[permanent dead link]
- ↑ Toyin Falola (1998). Violence in Nigeria: the crisis of religious politics and secular ideologies. University Rochester Press. p. 159. ISBN 1-58046-018-6.