Birgediya-Janar John Atom Kpera (An haife shi a ranar 3 ga watan Janairun shekarar 1941) ya kasance Gwamna Soja na farko a Jihar Anambra a Nijeriya daga Maris 1976 zuwa Yulin 1978, bayan an kirkireshi daga tsohuwar Jihar Gabas ta Tsakiya a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo. Daga baya ya kasance Gwamnan Soja na Jihar Benuwai daga Janairun shekarata 1984 zuwa Agustan shekarar 1985 a lokacin mulkin soja na Manjo-Janar Muhammadu Buhari.[1]

John Kpera
Gwamnan jahar benue

ga Janairu, 1984 - ga Augusta, 1985
Aper Aku (mul) Fassara - Jonah David Jang
Gwamnan jahar Anambra

ga Maris, 1976 - ga Yuli, 1978 - Datti Abubakar
Rayuwa
Cikakken suna John Kpera
Haihuwa 3 ga Janairu, 1941 (83 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Tiv
Harshen uwa Harshen Tiv
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Tiv
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar

Farkon Rayuwa

gyara sashe

An haifi John Atom Kpera a ranar 3 ga watan Janairun shekarar 1941 a Mbatierev, karamar hukumar Gboko a cikin jihar Benuwai ta yanzu. Ya halarci Kwalejin Katsina-Ala, yanzu ta zama Kwalejin Gwamnati ta Katsina-Ala, (1956–1961) don karatun sakandare. Bayan ya shiga aikin soja ya halarci Makarantar Koyon Soja ta Haile Selasie, Habasha a shekarar 1962 domin horar da shi kan aikin soja, kuma an ba shi mukamin Laftana na 2 a kungiyar Injiniya a shekarara 1965. Ya rike mukamai da mukamai daban-daban da suka hada da Injiniya Brigade Commander, Kwamandan Squadron, Regimental Commander, da Kwamanda, Corps of Engineers.

Aikin Soja

gyara sashe

Ya taka rawa a juyin mulkin soja na farko a Najeriya a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, inda ya taimakawa Chukwuma Kaduna Nzeogwu a yunƙurin kifar da gwamnatin yankin Arewa. Juyin mulkin bai yi nasara ba a manufofinta, amma ya haifar da Manjo-Janar Johnson Aguiyi-Ironsi wanda ya hau mulki a gwamnatin soja ta farko ta Najeriya.

An naɗa shi Gwamnan Soja na Jihar Anambra daga watan Maris shekarar 1976 zuwa watan July shekara ta 1978, a lokacin mulkin soja na Olusegun Obasanjo. Daga nan kuma ya zama Kwamandan Makarantar Sojoji ta Hedikwatar injiniyoyi, sannan Daraktan Manpower, Hedikwatar Sojojin Nijeriya ya biyo baya.

A ranar 4 ga watan Janairun shekarar 1984 aka nada shi Gwamnan Soja na Jihar Benuwai, shugaban soja na farko da aka haifa a jihar da ya mulki jihar. Ya kirkiro wata manufa ta tilastawa mutane tsabtace muhallinsu karkashin kulawar sojoji, aikin da magadansa suka kiyaye. A lokacin da aka sauke shi daga mukaminsa na gwamna, ya ce game da baitul malin jihar ya bar shi fanko domin ya sadu da shi fanko.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. http://www.worldstatesmen.org/Nigeria_federal_states.htm
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-03. Retrieved 2021-07-25.