Audu Bako
Audu Bako Tsohon kwamishinan yan sanda ne Mai ritaya, an kuma haife shi a shekara ta alif 1924, Shine gwamnan farko na jihar Kano, Nijeriya a lokacin mulkin soja na General Yakubu Gowon bayan kafuwar jahar daga yankin Arewacin Najeriya.
Audu Bako | |||
---|---|---|---|
Mayu 1967 - ga Yuli, 1975 - Sani Bello → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jahar Kaduna, 24 Nuwamba, 1924 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Hausawa | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Mutuwa | Jahar Kaduna, 1980 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa, Manoma da Ƴan Sanda | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Tarihin sa
gyara sasheAn haifi Audu Bako a shekarar 1924 a Barikin yan sanda dake Kaduna. Mahaifinsa yayi aikin dan sanda na tsawon shekaru 36. Audu yayi karatu a Makarantar Kaduna Government School da kuma Zariya Middle School. Bako ya shiga aikin dansanda a 1942. [1]
Gwamnan Jihar Kano
gyara sasheAn kuma naɗa shi a matsayin Gwamnan Jihar Kano a lokacin tshohuwar jahar ta Kano a shekarar 1967 lokacin mulkin soja. Bako yayi aiyukan raya kasa sosai a jahar ta kano. A shekarar 1969 ya fara gina madatsar ruwa ta Bagauda. Tsakanin 1970-1973 gwamnatinsa ta gina babbar madatsar ruwa ta Tiga, domib bunkasa harkar Noma. Aikinsa na samar da ruwansha na Timas Danbatta ya tsaya, har sai a shekarar 2008 sannan aka karasa shi inda ake samar da ruwan sha ga kananan hukumomin Dambatta, Makoda da Minjibir.
Rayuwar sa
gyara sasheAudu Bako yayi ritaya a shekarar 1975 lokacin mulkin retired a shekarar 1975 Murtala Muhammed inda ya kama aikin noma a jahar Sokoto. Ya rasu a shekarar 1980 yabar mata da yaya 11. Bayan rasuwar sa an sauya ma matsar ruwa ta tiga zuwa sunan [2] Audu bako yasha samun kyaututtuka a wasannin kwallon doki (wato Polo). Ana matukar girmama Audu Bako sosai.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ John N. Paden, Religion and political culture in Kano, University of California Press, 1973, ISBN: 0-520-01738-2, p. 339.
- ↑ Raph Uwechue, Africa who's who, Volume 1, Africa Journal Ltd. for Africa Books Ltd., 1981, ISBN: 0-903274-14-0, p. 71.
- ↑ Beverly Blow Mack, Muslim women sing: Hausa popular song, Indiana University Press, 2004, ISBN: 0-253-21729-6, p. 66.