Manoma jam'in kalma ce ta manomi sannan kalmar ta samo asali ne daga Noma Su manoma suke noma dukkan kayan masarufi na abinci kamar irinsu hatsi, borkono, tarugu, tumatur, tattasai, alaiyaho, kabeji, latas da dai sauran su. Manoma sun kasu zuwa kashi biyu ne. Akwai masu noman rani akwai kuma masu na Damana da kuma na zamani duk da dai yanzu kusan duka manoma suna amfani da kayayyakin zamani. Sai dai wani lokacin manoma suna fuskantar kalubale da matsalolin rashin kayan aiki da don saboda rashin tallafin daga gomnati zaka hasashe ya nuna kaso kusan saba'in (70) cikin ƴan Najeriya manoma ne amma saboda babu cikakkun kayan aiki da tallafi shi yasa harkokin noma ba su bunƙasa ba.[1]

Wikidata.svgManoma
sana'a
04-09-12-Schaupflügen-Fahrenwalde-RalfR-IMG 1232.jpg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na agricultural worker (en) Fassara
Field of this occupation (en) Fassara Noma
ISCO-88 occupation code (en) Fassara 6111 da 9212
manomi yana huɗa da galmar shanu a cikin gona

Nau'in manomaGyara

1- Manoman Kasuwanci.

2- Manoman Infaki.

Su manoman kasuwaci suna nomane sabida su sayar wa yan kasuwa bayan sun girbe abinda suka noma imma dai hatsi ko makamacin haka domin su samar wa kasu da iyalansu kudin shiga don more rayuwa. yawancin yan wainnan bangaren mutanen birni ne, amman suna amfani ne da kudinsu su biya mutanen kauye sai suyi musu aikin noman kodai lokacin rani ko na damun.

Manoman Infaki, duk ita kalmar Infaki kalmar larabci da ta ginu daga 'Anfaka, Yunfiku, Infaakan'

wace take nufin abun da aka kashe na kudi ko aka ciyar, manoman Infaki su suna yi noma ne saboda ciyar da iyalansu kawai. Sannan suna yin noma ne kan gwargwadon abunda iyalansu zasu ci kuma su taimaki wasu,

ManazartaGyara

  1. https://www.bbc.com/hausa/news/story/2010/03/100302_foodseries_farmers