Umaru Shehu
Umaru Shehu (An haife shi ne a ranar 8 ga watan Disamba, a shekarar 1930), ya kasan ce shi ne farfesa a likitancin Nijeriya kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Nijeriya, Nsukka. Ya kasance Farfesa Emeritus, lafiyar al'umma, Jami'ar Maiduguri kuma tsohon Shugaban Kwalejin Kimiyya ta Najeriya.
Umaru Shehu | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Maiduguri, 8 Disamba 1930 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Mutuwa | Maiduguri, 2 Oktoba 2023 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Malami da Farfesa | ||
Employers |
Jami'ar Najeriya, Nsukka Jami'ar Ahmadu Bello | ||
Kyaututtuka |
gani
| ||
Mamba | Makarantar Kimiyya ta Najeriya |
Farfesa Umaru ya sami digiri na farko na likitanci, MBBS daga Jami'ar London. Farfesa Umaru Shehu ba kawai shahararren farfesa ne a likitancin Najeriya ba, dattijo ne.[1][2]
Rayuwa
gyara sasheA jami'ar Bayero, Kano, an nada shi Pro-kansila da kuma shugaban majalisar gudanarwa, daga a shekarar 1993-1996,[3] sannan kuma ya ninka matsayin Pro-kansila da shugaban kwamitin gudanarwa na jami'ar ta Lagos, daga shekarar 1996-1997.[4][5] Ya yi aiki a matsayin memba na kwamitoci da yawa, kansiloli, ɓangarori dakuma kwamitocin a matakin kasa da na duniya.
Farfesa Umaru Shehu ya kasance shugaban makarantun koyon aikin likitanci a Afirka, daga shekarar 1973-1975; kuma mai nazarin waje na kiwon lafiyar jama'a, jami'ar makarantar likitanci ta Ghana. Shine shugaban kwamitin gwamnoni na yanzu na kungiyar STOPAIDS; shugaban hukumar kula da cutar kanjamau ta ƙasa, (NACA)]. Ya kuma sami haɗin gwiwa na Cibiyar Nazarin ciwon Kansa.
Manazarta
gyara sashe- ↑ M.D.Aminu (7 September 2019). "Professor Umaru Shehu". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 30 June 2023.
- ↑ "Professor Emeritus Umaru Shehu CFR". IHV NIGERIA.org (in Turanci). Retrieved 30 June 2023.[permanent dead link]
- ↑ "Popular Nigerian academic, Umaru Shehu, is dead". Premium Times. 2 October 2023. Retrieved 4 October 2023.
- ↑ Auyo, Aisha (18 August 2018). "Prof Umaru Shehu: life and times of Nigeria's foremost academic guru". Neptune Prime (in Turanci). Retrieved 30 June 2023.
- ↑ Babah, Chinedu (20 March 2017). "SHEHU, Prof. Emeritus Umaru". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 30 June 2023.