Jami'ar Najeriya, Nsukka

Jami'a

Jami'ar Najeriya, da turanci University of Nigeria Nsukka ko kawai UNN, jami'ar gwamnatin Tarayyar ce dake a garin Nsukka, Jihar Enugu, Nijeriya. Nnamdi Azikiwe ne ya kafa ta a shekarar 1955, amma an buɗe ta ne a 7 ga watan Oktoban 1960, Jami'ar Nijeriya nada rassa uku – a Nsukka, a Enugu, da kuma a Ituku-Ozalla – wadanda dukkanin rassan suna nan ne a jihar Enugun Nijeriya.

Jami'ar Najeriya, Nsukka

To restore the dignity of man
Bayanai
Suna a hukumance
University of Nigeria, Nsukka
Iri jami'a da open-access publisher (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Laƙabi Lion and lionesses
Aiki
Mamba na Ƙungiyar Jami'in Afrika
Harshen amfani Turanci da Harshen Ibo
Adadin ɗalibai 23,815
Mulki
Hedkwata Enugu
Tarihi
Ƙirƙira 1955
Wanda ya samar

unn.edu.ng


Jami'ar itace jami'a ta farko na kasa, wacce aka tsara ta akan irin tsarin karatun kasar Amurka. Tana kuma daga cikin manyan jami'a biyar a Nijeriya. Kuma jami'a ta farko dake da land-grant university a Afirka. Jami'ar nada tsangayoyin Ilimi guda 15 da sashe na bangarorin karatu guda 102. Jami'ar na gudanar da kwas na karatuka guda 82 na masu digirin farko da kuma guda 211 na masu digiri na gaba.[1]

Jami'ar ta gudanar da murnar cikar ta shekaru 50th da kafuwa a watan Oktoban shekarar 2010.

Manazarta gyara sashe

  1. University of Nigeria. Unn.edu.ng. Retrieved on 17 October 2011.