Dikko Umaru Radda

Ɗan siyasan Najeriya
(an turo daga Umar Dikko Raɗɗa)

Dr. Dikko Umaru Radda (an haife shi a ranar 10 ga watan satumba, a shekara ta alif ɗari tara da sittin da tara (1969A.C) Miladiyya a karamar hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina. Dan siyasa ne, shine zababben gwamnan Jihar katsina a karkashin jam'iyyar APC a babban zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Mayu na shekarar 2023 inda yayi nasara ne da Kuri'u 859,892.[1] Shine Darakta Janar/Babban Babban Jami’in Hukumar Raya Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN).[2]

Dikko Umaru Radda
gwamnan jihar Katsina

2023 -
Aminu Bello Masari
Rayuwa
Haihuwa Dutsin-Ma, 1970 (53/54 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa
(1992 - 1996)
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Mai tattala arziki
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
hoton dikko radda

Tarihi:Yusuf sahabi bdl

Dikko Umar Radda ya fara karatunsa na farko a makarantar firamare ta Radda daga Shekara ta 1974 zuwa 1980. Daga nan ya wuce zuwa Kwalejin Malamai ta Zariya tsakanin shekara ta 1980 zuwa 1985.[3] Ya shiga Kwalejin Ilimi ta Kafanchan a shekara ta 1986 zuwa 1990, inda ya samu takardar shaidar NCE. Ya shigaJami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi a shekara ta 1992 zuwa 1996, inda ya kammala karatunsa na B-Tech.Agric Economic and Extension (Hons). Daga nan kuma ya sami admission a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria a shekara ta 1998 zuwa 2004 inda ya samu MSC Agric Extension and Rural Sociology a shekara ta 2004.[4] Ya koma ABU Zariya a shekara ta 2005 don samun digiri na biyu a fannin harkokin kasa da kasa da diflomasiyya. Ya kammala karatunsa na digirin digirgir (P.h.D) a fannin aikin gona da ilimin zamantakewar karkara a shekara ta 2015.

Aiki da Siyasa

gyara sashe

Dikko Umar Radda ya kasance malamin makaranta tsakanin 1989-1999. Ya yi aiki a matsayin ma'aikacin banki tare da rusasshiyar bankin duniya na FSB tsakanin shekarar 1999-2003. [5]

Yayi Shugabancin Karamar Hukumar Charanchi ta Jihar Katsina tsakanin Jan 2005 zuwa Afrilu 2007. kuma sannan an nada shi Shugaban Kwamitin riko na Karamar Hukumar Charanchi, a watan Mayun shekarar 2007. Sauran mukaman daya rike akwai; Babban Mai Taimakawa 'Yan Majalisu, NASS, Abuja, 2012-2014, Sakataren Jin Dadin Jama'a (APC), Yuni 2014-Yuli 2015. Ya rike sarautar gargajiya ta Gwagwaren Katsina a masarautar KatsIna an nada shi a matsayin shugaban ma’aikata na Gwamnan Jihar Katsina. Shi ne Darakta Janar/Babban Babban Jami’in Hukumar Raya Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN).[6] Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Dr Dikko Umaru-Radda karo na biyu a matsayin shugaban Hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana'o'i a Najeriya wato SMEDAN. Sanarwar ta fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a wata takarda mai dauke da kwanan watar 12 ga watan Maris na 2021.

 
Dikko Umaru Radda a tsakiya

Dr. Dikko Umar Radda ya shiga siyasar neman kujerar Gwamnan Jihar Katsina, a siyasar 2023. A daidai lokacin ne ya ajiye shugaban Hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana'o'i a Najeriya wato SMEDAN, a ranar Laraba, 1 ga watan Yuni 2022, inda ya damka wa Mr Wale Fasanya mukamin, bayan ya lashe zaben fidda gwanin takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin jam'yyar APC.

Zaben Gwamna na 2023

gyara sashe

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ayyana Dokta Umar Radda na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina. Radda ya samu nasara ne da ƙuri'u 859,892, yayin da mai biye masa Garba Yakubu Lado Danmarke na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a 486,620. Jami'in da ke tattara sakamakon zaɓen gwamnan a jihar ta Katsina, Farfesa Mu'azu Abubakar Gusau ne ya bayyana sakamakon a daren Lahadi. Jihar Katsina ita ce jihar shugaban Najeriya Muhammad Buhari. An Rantsar da Dr Dikko Radda a Matsiyin wadda ya Lashe zabe a Ranar Litinin a Shirin da Tare ga wata Mayu She kara ta Dubu biyu da a shirin da Ukku [7]


Manazarta

gyara sashe
  1. "Dikko Radda na APC ya lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina". BBC Hausa. 19 March 2023. Retrieved 20 March 2023.
  2. "Tattaunawa ta musamman da Shugaban SMEDAN, Dr Dikko Umar Radda". Manhajar Blueprint Hausa. 13 August 2021. Retrieved 20 March 2023.
  3. https://hausa.legit.ng/1408063-buhari-ya-sabunta-na-umaru-radda-a-matsayin-shugaban-smedan.html
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-11-28. Retrieved 2021-12-09.
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-12-09. Retrieved 2021-12-09.
  6. https://www.bbc.com/hausa/53295828
  7. https://www.bbc.com/hausa/articles/c901lvv4p48o