Thomas Aguiyi-Ironsi ɗan siyasar Najeriya ne kuma jami'in diflomasiyya wanda a baya ya taɓa riƙe muƙamin ƙaramin ministan tsaro. Ɗan tsohon shugaban mulkin soja ne Manjo Janar Johnson Aguiyi-Ironsi,[1] kuma shi ne jakadan ƙasar Togo kafin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya naɗa shi ya gaji Roland Oritsejafor a matsayin ƙaramin ministan tsaro.[2] Aguiyi-Ironsi daga Umuahia ne a jihar Abia.[1]

Thomas Aguiyi-Ironsi
Ministan Tsaron Najeriya

30 ga Augusta, 2006 - 26 ga Yuli, 2007
Rabiu Kwankwaso - Yayale Ahmed
ambassador of Nigeria to Togo (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Jahar Kaduna
ƙasa Najeriya
Ƙabila Tarihin Mutanen Ibo
Harshen uwa Harshen, Ibo
Ƴan uwa
Mahaifi Johnson Aguiyi-Ironsi
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya
agwui ironsi

Yayin da Aguiyi-Ironsi ke zama jakada a Togo, an taƙaita zaɓin da zai maye gurbin ministar harkokin wajen ƙasar mai barin gado, Ngozi Okonjo-Iweala, shi da Joy Ogwu.[1] Sai dai bayan da Obasanjo ya kori Oritsejafor, Aguiyi-Ironsi ya samu muƙamin ministan tsaro yayin da Ogwu ya zama ministan harkokin waje. An rantsar da su biyu a ranar 30 ga Agusta 2006.[2]

A ranar 24 ga Janairu, 2007, Aguiyi-Ironsi ya ba da sanarwar cewa Najeriya za ta aika da bataliyar sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Somaliya.[3]

Manazarta

gyara sashe
Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe