Nigerian Railway Corporation hukuma ce ta zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya.

Nigerian Railway Corporation

Bayanai
Gajeren suna NRC da NR
Iri railway company (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Aiki
Ma'aikata 6,516
Mulki
Hedkwata Abuja da Lagos,
Tsari a hukumance state-owned enterprise (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1912
1898
Wanda yake bi Lagos Government Railway (en) Fassara da Baro-Kano Railway (en) Fassara
nrc.gov.ng
Reshen kamfanin a Ibadan
Tashar jirgin Kasa na Kamfanin a Minna
Nigerian Railway Corporation

An kirkiri Nigerian Railway Corporation a 1898 lokacin da turawan mulkin mallaka suka samar da hanyoyin jiragen kasa na farko a Nigeria. A October 3, 1912, hukumar jiragen kasa ta Lagos da kuma hukumar jiragen kasa ta Baro-kano suka yi yarjejeniya ta yin hadaka da juna yayin da suka fadada zirga-zirgar su ta zama ta duniya gaba daya wanda kuma suka canja suna zuwa Government Department of Railways. A shekara ta 1955 aka sake canjawa Kamfanin suna izuwa sunan sa na yanzu wato Nigerian Railway Corporation tareda samun cikakkiyar dama ta gudanar da zirga-zirgar su a ko Ina a fadin Nigeria.

Kamfanin ya samu daukaka sosai jim kadan bayan samun yanci a 1964. Bayan wannan lokacin NRC sun sami wata barazana ta ci baya da kuma tabarbarewar kayan aiki na wani lokaci Mai tsawo. Hukumar ta samu karyewa a shekara ta 1988 wanda har takai ga dakatar da zirga-zirga tsawon wata shida. Daga nan aka gyara hanyoyin jiragen a shekara ta 2002 Kuma jiragen suka dawo aiki gadan-gadan kamar a baya. Kamfanin ya sake samun matsaloli daga baya har zuwa 2006 inda aka sake yin gyararrakin hanyoyi da kuma samar da sababbin tsare-tsare abisa taimakon kasashen waje.

NRC ta sami matsaloli na karayar tattalin arziki fiye da sau daya a shekara ashirin da ta gabata. Rashin inganta kayan aiki da kuma yawan ma'aikata ya bada gudun mawa wajen karyewar kamfanin. A shekara ta 2015 bayan wasu tsare-tsare da akai tayi an takaita zirga-zirgar jiragen izuwa sau hudu a sati, zuwa Kano sau biyu, zuwa Jos sau daya da Kuma zuwa Maiduguri sau daya.

Manazarta

gyara sashe