Nigeria National Democratic Party

Jam'iyyar siyasa ta farko a Najeriya.

Jam'iyyar National Democratic Party ( NNDP ) ita ce jam'iyyar siyasa ta farko a Najeriya.

Nigeria National Democratic Party
Bayanai
Iri jam'iyyar siyasa
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 1922

Tarihi gyara sashe

Herbert Macaulay ne ya kafa ta a shekara ta 1923 don cin gajiyar sabon Kundin Tsarin Mulki na Clifford, wanda ya gaji Majalisar Najeriya ta 1914. Jam’iyyar NNDP ta yi nasarar shirya ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki a Legas a matsayin ƙungiya ɗaya wacce ta iya yin takara a siyasance. Jam'iyyar (NNDP) ta tsayar da 'yan takara da dama domin neman kujeru a zaɓen shekarar 1922 na majalisar dokokin Legas, inda ta samu kujeru uku. Jam'iyyar ta lashe dukkan kujeru a zaɓukan 1923, 1928 da 1933. Ko da yake, babban aikin jam'iyyar shi ne sanya 'yan takara a cikin majalisar dokoki, tana da babbar manufa ta inganta dimokuradiyya a Najeriya, da kara yawan shiga Najeriya a cikin zamantakewa, tattalin arziki da ci gaban ilimi na Najeriya. Jam’iyyar ta ci gaba da mamaye harkokin siyasa a Legas har zuwa shekarar 1938, lokacin da kungiyar matasan Najeriya (NYM) ta mamaye ta a zaɓe.

Samuel Akintola ne ya karbe sunan jam’iyyar a shekarar 1964 ga jam’iyyarsa a wani mataki na kawar da jam’iyyar Action Group mai ra’ayin riƙau ƙarƙashin jagorancin Obafemi Awolowo daga mulki a yankin Yamma.[1][2]

Daga baya ɗan jam’iyyar Augustus Akinloye ya zama shugaban jam’iyyar ta kasa a shekarar 1978.

Nassoshi gyara sashe

  1. Martin Meredith, The Fate of Africa: A History of Fifty Years of Independence (Public Affairs Publishing: New York, 2005) p. 196.
  2. "Transforming Nigerian Party System". The Tide. Retrieved November 30, 2014.