Sa'adu Abubakar
An haifi mai martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'adu Abubakar III a 24 ga watan Agusta na shekara ta Alif da Dari tara da hamsin da shidda (1956), a sananniyar masarautar nan ta gidan sarkin musulmi dake Sakkwato a Arewacin Najeriya).
Sa'adu Abubakar | |||
---|---|---|---|
2 Nuwamba, 2006 - ← Muhammadu Maccido | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jahar Nasarawa Sokoto, 24 ga Augusta, 1956 (68 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Mutanen Fulani | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Siddiq Abubakar III | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Kwalejin Barewa Jami'ar Tsaron Nijeriya | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | soja | ||
Digiri | Janar | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Shi ne kuma ke riƙe da mukamin shugaban kungiyar Musulmi ta Najeriya wato (Jama'atu Nasril Islam, (JNI)). Bayan sarautar kasar Sakkwato kuma shi ne shugaban sama da mutane miliyan saba'in na musulman Najeriya wadanda sune suke sama da rabin mutanen Najeriya. Mai martaba Sa'adu Abubakar ya hau karagar mulki ne bayan rasuwar yayan sa wanda shi ne ke kan karagar kafin rasuwar sa wato Muhammadu Maccido, wanda ya rasu sakamakon hadarin jirgin sama daya rutsa dasu.
Manazarta
gyara sashe