Uche Ekwunife
Uche Lilian Ekwunife (née Ogudebe an haife ta a ranar 12 ga watan Janairun shekarar alif 1970), 'yar Siyasar Najeriya ce kuma memba a Majalisar Dattawan Najeriya ta 9 da ke wakiltar mutanen Anambra ta Tsakiya ta Sanatan ta Anambra kuma tana daya daga cikin matan sanatoci masu matukar tasiri a Majalisar.
Uche Ekwunife | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023 District: Anambra Central
ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 District: Anambra Central
5 ga Yuni, 2007 - 4 ga Yuni, 2015 District: Anambra Central | |||||||
Rayuwa | |||||||
Cikakken suna | Uche Lilian Ekwunife | ||||||
Haihuwa | Anaocha, Disamba 1970 (53/54 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
Nnamdi Azikiwe University Jami'ar Calabar | ||||||
Matakin karatu | Bachelor of Arts (en) | ||||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya Harshen, Ibo | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheEkwunife an haife ta a ranar 12 ga watan Disamba, shekarar alif 1970, a Igbo-Ukwu, Anambra ga Emmanuel da Lucy Ogudebe. Ekwunife ta halarci Jami'ar Calabar sannan ta kammala karatun ta na digiri a fannin kasuwanci da lissafi a shekarar alif 1993. Ta ci gaba da samun digiri na MBA daga Jami'ar Nnamdi Azikiwe a shekarar 2002.
Ekwunife ta yi aikin banki inda ta zama manajan yanki. Ta auri wani dan kasuwa daga yankin Nri[1] Anaocha LGA. Ita da Cif Larry Ekwunife suna da yara.[2]
Harkar siyasa
gyara sasheEkwunife ta tsaya zaben har sau biyu ba tare da nasara ba.[3] An zabe ta a matsayin wakiliya a shekarar 2007 don mazabar Anaocha/Njikoka/Dunukofia ta Anambra. Tana daga cikin mata 11 da aka zaba a 2007 wadanda aka sake zabarsu a 2011 lokacin da karamar majalisar ta kusan kashi 95% na maza. Sauran matan da aka zaba sun hada da Juliet Akano, Mulikat Adeola-Akande, Abike Dabiri, Nkiru Onyeagocha, Nnena Elendu-Ukeje, Olajumoke Okoya-Thomas, Beni Lar, Khadija Bukar Abba-Ibrahim, Elizabeth Ogbaga da kuma Peace Uzoamaka Nnaji.[4]
A 2015, an zabe ta a Majalisar Dattawan Najeriya. Tana daga cikin mata shida da aka zaba a Majalisar Dokoki ta 8. Sauran matan sun kasance Rose Okoji Oko, Stella Oduah, Fatimat Raji Rasaki, Oluremi Tinubu and Binta Garba.[5] Ekwunife ta ci zaben 2015 ne ta hanyar sauya sheka daga wata jam’iyyar siyasa zuwa waccan. Saboda wannan ne aka kalubalanci zabinta kuma a watan Disambar 2015, aka ayyana kujerarta babu kowa. Ekwunife ta kasa samun tsohuwar jam'iyyarta ta siyasa don mara mata baya a zaben cike gurbi na tsohon kujerar ta.[6]
Ta ci zaben sanata na 2019, mai wakiltar Anambra ta Tsakiya, Najeriya.[7][8] Ta sake yin irin wannan zaben a zaben majalisar dattijai na shekarar 2015, a Najeriya, amma ta sha kaye a hannun Sanata Victor Umeh.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kingdom of Nri". About Nri Kingdom.
- ↑ "About Uche Ekwunife - NASS". National Assembly of Nigeria.
- ↑ "The Independent National Electoral Commission (INEC)". INEC WEBSITE.
- ↑ "Women who will shape Seventh National Assembly". Vanguard News (in Turanci). 2011-06-06. Retrieved 2020-05-03.
- ↑ The 6 female senators in 8th National Assembly, Naij,com, Retrieved 15 February 2016
- ↑ APC panel disqualifies “fair-weather” Ekwunife from contesting Senate rerun on party's platform, 21 January 2016, Festus Owete, Retrieved 15 February 2016
- ↑ Ekwunife, Uche (February 28, 2019). "Finally,INEC Declares Ekwunife winner of Anambra central senatorial Election". This Day. Missing or empty
|url=
(help) - ↑ Ekwunife, Uche (November 9, 2018). "Nigeria Tribune". Missing or empty
|url=
(help)