Birgediya Mohammed Sani Sami ya kasance gwamnan jihar Bauchi, Nijeriya daga watan Janairun shekara ta alif ɗari tara da tamanin da hudu 1984A.c) zuwa watan Agusta shekarar 1985 a lokacin mulkin soja na Manjo Janar Muhammadu Buhari .

Mohammed Sani Sami
Gwamnan Jihar Bauchi

ga Janairu, 1984 - ga Augusta, 1985
Tatari Ali - Chris Abutu Garuba (en) Fassara
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Mons Officer Cadet School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Ɗan wasan polo

An haifi Mohammed Sani Sami a garin Zuru da ke cikin jihar Kebbi . Ya shiga aikin soja ne a ranar goma 10 ga watan Disamba na shekara ta 1962, kuma ya halarci kwasa-kwasan horo tare da Ibrahim Babangida . Ya kuma halarci Makarantar Mons Officer Cadet, Aldershot ( United Kingdom ), kuma an ba shi izini a ranar 25 ga watan Yuli, a shekara ta 1963. Janar Murtala Muhammed, shugaban kasa daga watan Yulin shekarar 1975 zuwa watan Fabrairu shekara ta 1976, ya nada Laftanar Kanar Sani Sami kwamandan Birged na Guards.

An nada Mohammed Sani Sami gwamnan jihar Bauchi bayan juyin mulkin 31 ga watan Disamban shekara ta 1983 wanda ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki. Ya rike ofis har zuwa watan Agustan shekara ta 1985, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya karbi mulki daga Buhari. Ya inganta cibiyoyin kiwon lafiya, kuma ya gudanar da wani babban shirin bunkasa harkar noma mai suna "dawo kasa". A lokacin gwamnan sa an gudanar da gasar kwallon hannu ta duniya a jihar Bauchi.

A watan Oktoba na shekarar 1984, yana fuskantar sabon rukuni na tsattsauran ra'ayin addini, ya yi gargadin cewa hana yin wa'azin addini a sarari yana nan daram. Ya kuma bayyana cewa shawarar rusa wasu majami'u mabiya addinin kirista don samar da hanyar sabuwar hanyar zobe ba wata hanya ce da za a kai hari kan wannan addinin ba, kuma ya ce gwamnati ta ware fili domin aikin Katolika don gina sabon coci.

Muhammadu Sani Sami ya yi ritaya a matsayin babban hafsa a ranar 3 ga watan Satumba a shekara ta 1990. Daga baya ya zama Sarkin Zuru, a jihar Kebbi, Nigeria.

1.Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-01-12. 2. Nowa Omoigui. "Military Rebellion of July 29, 1975: The Coup Against Gowon - Epilogue". Dawodu. Retrieved 2010-01-12. 3. "Past Executive Council: Brigadier Mohammed Sani Sami (1983 – 1985)". Bauchi State Government. Archived from the original on 2011-07-25. Retrieved 2010-01-12. 4. Abunakar Buhari. "Religious Fanatics Said Gaining Ground" (PDF). Kano Sunday Triumph. Retrieved 2010-01-12.

Manazarta

gyara sashe