Abubakar Tatari Ali (c. 1929 - 28 May 1993) an zaɓe shi Gwamnan jihar Bauchi, dake Nijeriya a shekara ta 1979, yana rike da mukami har zuwa juyin mulkin soja a ranar 31 ga Disamba ta shekara ta 1983 wanda ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki.[1]

Tatari Ali
Gwamnan Jihar Bauchi

Oktoba 1979 - Disamba 1983
Garba Duba - Mohammed Sani Sami
Rayuwa
Haihuwa 1929
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Tarayyar Amurka, 28 Mayu 1993
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Acikin shekara ta 1971, Ali Tatari ya kasance shugaban ma’aikatar yada labarai. Ya ziyarci Washington dake kasar Amuruka( D.C.), a waccan shekarar a yayin shirye-shiryen shirya bikin baƙar fata da al'adu na duniya, wanda za a yi a jahar Legas a cikin a shekara ta1974.

Siyasa da aiki

gyara sashe

An zabi Ali a shekara ta1979 a farkon Jamhuriya ta Biyu ta Najeriya a karkashin jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN). Gwamnatinsa ta himmatu wajen gina hanyoyi, ayyukan gidaje da masana’antu, sannan ta bude gonaki samfurin 16 a fadin jihar Bauchi. Ya fara kuma gina katafaren Otal din Zarand mai tauraro biyar. Ya kirkiro kananan hukumomi 43 a fadin jihar, wadanda daga baya aka soke su bayan juyin mulkin 31 ga watan Disambar shekara ta1993 wanda ya kawo sabuwar gwamnatin soja.

Ali ya yi ƙoƙari ya sake farfaɗo da masana'antar Nama ta Bauchi, ya kafa sabbin kayan aiki kamar Gubi [[Dairy Farm]], Madangala Sheep Ranch, Galambi Cattle Ranch da Gombe da Takko gonakin kaji. Waɗannan kamfanonin, waɗanda ma'aikatan gwamnati ke gudanarwa, gabaɗaya ba su da riba.

Manazarta

gyara sashe