Laylah Ali Othman
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Laylah Ali Othman(an haife ta a ranar 29 ga watan Janairu shekarata alif dubu daya da dari Tara da tamanin da shida (1986)) yar Najeriya ce wace aka fi sani da yin sana’ar sayar da kayan gyaran gida kamar kujeru da gadaje[1].Ita mawallafiya ce, kuma kuku ce[2],sanan kuma itace mamallakin kamfanin buga mujallar da ake kira L magazine, tana kuma gabatar da shiri da ake kira Voices of the Youth[3].
Laylah Ali Othman | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jihar Yobe, 29 ga Janairu, 1986 (38 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Maiduguri ESCAE-University, Benin (en) |
Harsuna |
Hausa Turanci Pidgin English (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan kasuwa, marubuci da mai gabatarwa a talabijin |
Farkon Rayuwa
gyara sasheAn haifa Laylah a jihar yobe[4], ammata tashi ne a Kaduna, inda tayi rayuwar ta a jihar Kaduna, inda tayi karatun ta na nursery da firamare a cikin Jihar Kaduna, Bayan kuma ta yi makarantar sakandire ta Junior & Senior a Damaturu. A halin yanzu ita ce Shugaba kuma Manajan Darakta na Superb rb , wato &N (Laylah & Nahaar) Interiors and Exterior Décor Nig[5].
Makaranta
gyara sasheTa na da Digiri a fannin harshen Ingilishi daga [6] Jami'ar Maiduguri, Diploma a interior decoration daga Lotus Educational Institute, Dubai da wani diploma kuma a space management daga Maren School of Interior Décor and Design, bugu da ƙari ta ƙara digiri na biyu a jami’ar ESAE dake ƙasa Benin Republic.
Aure
gyara sashetayi aure Sau biyu auren na mutuwa.
[7]Sana'a
gyara sasheLayla Ali othman ita ce ta ƙirƙiro da wani ƙungiya mai zaman kanta mai suna Laylah Initiative for the Boy and Girl Child Charity Foundation (LIBGC); ƙungiya ce da'ake ba da kulawa ga al-Manifī'', da kuma basu ilimi kyauta a wani rukuni na ɓangaren yaran da ke cikin buƙata, kamar Almajiri' da sauran ƙananan yara marassa galihu, ta hanyar shirin talabijin da ake kira Laylah's Way, inda take taimakan talakawa da kuma sauran jama'a, tana amfani da wanan shirin don taimakawa mutanen da ba zasu iya samun saukin rayuwa ko samun rayuwa mai kyau ba, ta hanyar basu cikakkiyar kayan gida[8].
Daga baya ta zama mai gabatar da shiri wanda ake kira Voices of the Youth. A cikin wannan shiri, ta bayar da damar samar da ingantacciyar rayuwa ga marasa galihu, da kuma karfafama mutane gwiwa game da yadda za su zama ƴan kasuwa, tare da koya masu ilimin yadda ake gina ingantaccen hanyar samun kuɗi, da kuma magance matsalolin da matasan Najeriyar ke fuskanta a yayin da suke ƙoƙarin samun ci gaba da nasara a rayuwarsu[9].
Bayan nasarorin da ta samu a kafafen yaɗa labarai, ita ce mai gabatar da shirin talabijin da ake kira Muryar Jama’a, shirin wasa ne wanda ke nuna rayuwa da al'adun Hausawa, Ita kuma ta mallaki kamfanin L Magazine, mujallar ce da ke nuna abubuwan kaman kayan ado na cikin gida, kiwon lafiya da salon rayuwa; ita ce marubuciya na Something Deep da Masked[10].
Lambobin yabo da nasarori
gyara sasheShekara | Lambar yabo | Kungiyar |
---|---|---|
2018 | Award of Excellence | Gamji Students |
2015 | Award of Honor | Eastern Mediterranean University (Nigerian Week) |
2018 | Award of Excellence | Department of Public Admin, Faculty of Admin, ABU |
2018 | Award of Excellence | West African Students |
2019 | Meritorious Award of Honor | Nigerian Youth Progress in Democracy |
2019 | Certificate of Honor | Democratic Youth Assembly of Nigeria |
2018 | Certificate of Appreciation | [permanent dead link] Startup Sokoto |
2018 | Certificate of Participation | Startup Kano |
2019 | Award of Honor | National Association of Nigerian Students (Zone A) |
2019 | Life Time Award of Credence | Youth Assembly of Nigeria |
2019 | Northern Philanthropic Award of Excellence | Save Democracy Group, Africa |
2020 | Award of Honor | National Association of Northern Corpers[11] |
2019 | Corporate Social Responsibility Award | PR Times Africa[permanent dead link] |
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-49865877?ocid=wshausa.chat-apps.in-app-msg.whatsapp.trial.link1_.auin
- ↑ http://www.landnkitchen.com/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-04-22. Retrieved 2020-05-19.
- ↑ https://www.youtube.com/watch?v=CGkA-Onzamc
- ↑ http://www.superblandninteriors.com/[permanent dead link]
- ↑ http://www.citypeopleonline.com/meet-the-young-female-entrepreneurs-rocking-abuja/
- ↑ https://hausa.legit.ng/1263425-bayan-aurena-ya-mutu-sau-biyu-mutane-suna-ta-zargin-cewa-lalacewa-zanyi-laila-ali-othman.html
- ↑ https://www.youtube.com/watch?v=RxDy0lXAY2A&feature=youtu.be
- ↑ http://www.citypeopleonline.com/meet-the-young-female-entrepreneurs-rocking-abuja/
- ↑ https://www.youtube.com/watch?v=CGkA-Onzamc
- ↑ https://www.youtube.com/watch?v=CGkA-Onzamc