Lawal Kaita

Dan siyasar Najeriya

Lawal Kaita (An haife shi ne a ranar 4 ga Watan Oktoban shekarar 1932) na Miladiyya (A.C) Ya kuma mutu ne a ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2018). Ya kasan ce ɗan siyasan Najeriya ne da aka zaba a jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN) a matsayin gwamnan jihar Kaduna, Najeriya, ya rike mukami tsakanin Oktoba zuwa Disamban 1983, lokacin Jamhuriyya ta biyu ta Najeriya wacce ta kare da juyin mulkin da ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki.[1][2][3]

Lawal Kaita
gwamnan, jihar Kaduna

Oktoba 1983 - Disamba 1983
Abba Musa Rimi - Usman Mu'azu
Rayuwa
Haihuwa Jahar Katsina, 4 Oktoba 1932
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Abuja, 2 ga Janairu, 2018
Yanayin mutuwa  (liver failure (en) Fassara)
Karatu
Makaranta Kwalejin Barewa
London School of Economics and Political Science (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
jarida akan lawal kaita

An haifi Lawal Kaita a ranar 4 ga Oktoban shekarar 1932 a Katsina, Arewacin Najeriya.[4] Shi ɗan uwan ​​Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ne na jini kuma dan gidan sarautar Nagogo, sarakunan gargajiya na masarautar Katsina. Ya halarci Kwalejin Barewa, Zariya (1946 - 19550) sannan daga baya ya yi karatu a Makarantar Tattalin Arziki ta London (1971–1972).. Bayan dawowarsa Najeriya, Kaita ya zama ma'aikacin gwamnatin jihar Kaduna. Ya yi aiki a matsayin Sakatare a Hukumar Ruwa ta Jiha (1973–1975), Kwamishinan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki (1975 - 1977) da Mataimakin Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka na Jihar Kaduna (1976–1977).[5][6][7]

Farkon rayuwa

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. Ademola Adeyemo (13 January 2009). "Where Are Second Republic Governors?". This Day. Retrieved 20 April 2010.
  2. "Now That Nigeria Is Ungovernable What Next?". Sahara Reporters. 2014-03-15. Retrieved 2018-03-06.
  3. "FACT: It Was PDP That Promised To Make Nigeria Ungovernable in 2011, Buhari Never Did!". Every Nigerian Do Something [ENDS] (in Turanci). 2014-08-04. Archived from the original on 2018-03-07. Retrieved 2018-03-06.
  4. "Those Behind SGBN Bank". ThisDay. 19 June 2003. Archived from the original on 23 January 2005. Retrieved 20 April 2010.
  5. Guardian News Ng. "Kaduna Ex-Governor Dies At 85". Archived from the original on 2021-03-04. Retrieved 2021-02-15.
  6. Premium Times Nigeria. "Lawal Kaita Defunct Kaduna State Ex-Governor Dies At 85".
  7. Femi Babafemi (9 June 2008). "I want Yar'Adua removed by Supreme Court – Lawal Kaita". Online Nigeria Daily News. Archived from the original on 27 February 2012. Retrieved 20 April 2010.