Kisan kiyashi a Buni Yadi, Fabrairu 2014
A ranar 25 ga watan Fabrairu, 2014, an kashe yara maza hamsin da tara (59), a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Buni Yadi a Jihar Yobe a Najeriya. An kuma ƙona gine-gine ashirin da huɗu na makarantar sakamakon harin. Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, amma a cewar kafafen yaɗa labarai da jami'an ƙasar ana zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai harin.[1][2]
| ||||
Iri | Kisan Kiyashi | |||
---|---|---|---|---|
Bangare na | Rikicin Boko Haram | |||
Kwanan watan | 25 ga Faburairu, 2014 | |||
Wuri | Jihar Yobe | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 59 |
Bayan fage
gyara sasheKwalejin Gwamnatin Tarayya makarantar kwana ce da ke Buni Yadi, wani gari a Jihar Yobe, Najeriya.[3] Makarantar haɗin guiwa da sakandare tana da gine-gine ashirin da huɗu a lokacin da aka kai harin.[4]
Tun a shekarar 2009 ne mayakan ke rikici da gwamnati a Arewacin Najeriya. Kungiyoyin ‘yan bindiga sun ƙara mayar da hankali wajen kai hare-hare kan fararen hula tun a watan Mayun 2013 lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan ya bai wa sojoji izinin kawar da ‘yan adawa. Rikicin ya haifar da ƙaruwar rashin zaman lafiya a Najeriya, wadda ke kan gaba wajen samar da man fetur a Afirka. A watan Fabrairun 2014, 'yan bindiga sun yi sanadin mutuwar mutane 300, galibi fararen hula. A karshen watan Fabrairu ne gwamnatin kasar ta rufe iyakar Najeriya da Kamaru a ƙoƙarin ta na hana ‘yan bindiga kai hare-hare a Najeriya sannan su tsere zuwa Kamaru.[4]
Ƙungiyar Boko Haram, wacce sunanta ke nufin "ilimin yammacin duniya zunubi ne", ta sha kai hare-hare a makarantu a lokuta da dama.[4] An bayyana ƙungiyar a hukumance a matsayin ƙungiyar ta’addanci a Najeriya da Amurka, kuma an bayar da tukuicin ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai ga kama shugabannin ƙungiyar. A jimilce, an danganta mutuwar sama da mutane 1,000 da Boko Haram tayi sanadiya tun daga watan Mayun 2013.[3] Ƙungiyar ta ƙona makarantu sama da 200 kamar yadda alƙalumma suka nuna.[5] Abubakar Shekau, wanda ake zargin shugaban ƙungiyar Boko Haram ne, ya fitar da wata sanarwa ta faifan bidiyo a tsakiyar watan Fabrairun 2014 inda ya yi alƙawarin ci gaba da yaƙin da ƙungiyar ke yi na yaki da kimar kasashen yamma tare da yin barazanar faɗaɗa hare-haren su na ta'adanci.[3]
Mako guda kafin kai harin, ƴan ƙungiyar Boko Haram sun kashe mutane 60 a garin Bama da ke jihar Borno mai makwabtaka; kwanaki huɗu kafin wannan harin, mayakan sun kashe mutane 106 a wani ƙauye mafi yawan mabiya addinin Kirista, Izghe; sannan makwanni uku kafin nan mayakan sun kashe mutane 78 a wasu hare-hare biyu da aka kai a yankin.[1]
Kai hari
gyara sasheA ranar 25 ga Fabrairu, 2014, ‘yan bindiga sun kutsa cikin Kwalejin Gwamnatin Tarayya a lokacin da daliban ke barci. Sun jefa bama-bamai a cikin dakunan kwanan dalibai yayin da suka kutsa dakunan riƙe da bindigogi. A cewar wani shaidan gani da ido, “daliban na ƙoƙarin hawa taga, sai ‘yan ta’addan suka yanka su kamar tumaki da suka sare makogwaronsu. An kashe wasu da suka gudu.”[3] Dukkan gine-gine ashirin da hudu sun ƙone kurmus yayin harin.[4]
An kashe yara maza hamsin da tara a harin. Wasu sun mutu sakamakon harbin bindiga ko raunukan wuka, yayin da wasu kuma suka ƙone kurmus.[4] An kai gawarwakin waɗanda suka tsira da ransu zuwa asibitin kwararru na Sani Abacha da ke babban birnin jihar Damaturu. Mai magana da yawun asibitin ya ce da alama mayakan sun ceci dalibai mata da gangan.[3]
Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, harin ya “bore the hallmarks” na ƙungiyar Boko Haram.[3] Jami’an yankin sun kuma danganta harin da kungiyar, amma ba a samu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin ba.[6]
Bayan haka
gyara sasheShugaba Goodluck Jonathan ya kira harin da aka kai Kwalejin Gwamnatin Tarayya da "Kisan banza da rashin hankali ... ta ‘yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayi waɗanda a fili suka rasa duk wata dabi’a ta ɗan Adam, suka juya zuwa ga halayar dabba”[4] Ya sha alwashin "kawar da bala'in ta'addanci har abada".[6] Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da harin yana mai cewa "babu wata manufa da za ta iya tabbatar da irin wannan tashin hankali" ya kuma ce ya damu matuƙa da ƙaruwar hare-hare da rashin tausayi.[5]
Ƴan uwan waɗanda harin ya rutsa da su sun kewaye ɗakin ajiyar gawa a fusace suna neman a ba su amsa. Sojoji sun mamaye ginin domin dawo da zaman lafiya.[3] Kasawar da gwamnati ta yi na hana kai harin Kwalejin Gwamnatin Tarayya da makamantansu ya janyo hasarar al’umma a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.[4] Ɗalibai a faɗin yankin sun ki kwanciya barci a makarantunsu na kwana bayan harin inda suka koma gidajensu.[5]
Dalili
gyara sasheGwamnatin jihar Yobe
gyara sasheA cewar gwamnatin jihar Yobe, sojojin da ke gadin wani shingen binciken ababan hawa da ke kusa da wurin da aka kai harin sun janye daga aiki sa’o’i kaɗan kafin harin.[3] Gwamnan jihar Ibrahim Gaidam ya ɗora alhakin janye sojojin da silar kai harin kuma ya ce sojojin ƙasar sun gaza wajen kare daliban.
Kakakin rundunar Soji
gyara sasheKakakin rundunar sojin ƙasar, ya ce tun da farko an tarwatsa shingen binciken a wani ɓangare na aikin rundunar hadin gwiwa. Ya ce lalata layukan waya, mai yiyuwa maharan su kayi, don hana sojoji jin labarin harin a lokacin da za su mayar da martani.[6]
Najeriya da Amurka
gyara sasheƘungiyar Boko Haram da ƙasar Najeriya da Amurka suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci, ana zargin hakan ce ta saka ƴan ta'adan fara kai harin a matsayin wani ɓangare na yakin da ta ke yi na samar da daular Musulunci[note 1] a yankin Arewacin Najeriya na Musulmi.[7][8]
Duba kuma
gyara sasheBayanan kula
gyara sashe- ↑ A kiyaye wannan iƙirarin nasu na samar da daular musulunci. Wannan ba koyarwa Addini musulunci suke yi ba face ta'adanci tsantsa
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Islamist Militants Blamed for Deadly College Attack in Nigeria". New York Times. 25 February 2014. Retrieved 6 March 2014.
- ↑ "Boko Haram kills 59 boys at Nigerian boarding school". The Guardian. 25 February 2014. Retrieved 6 March 2014.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 3.5 3.6 3.7 "Sleeping Students 'Killed By Boko Haram'". Sky News. February 25, 2014. Retrieved February 26, 2014.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 4.5 4.6 Hemba, Joe (February 25, 2014). "Nigerian Islamists kill 59 pupils in boarding school attack". Reuters. Archived from the original on October 31, 2016. Retrieved February 26, 2014.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 "Schools, university empty after deadly Nigeria attack". AFP. February 28, 2014. Archived from the original on March 4, 2014. Retrieved March 1, 2014.
- ↑ 6.0 6.1 6.2 "Nigerian Military: Phones Not Working At Time of School Attack". Voice of America. February 26, 2014. Retrieved March 1, 2014.
- ↑ Abubakar, Aminu (February 25, 2014). "43 killed in Nigeria in suspected Boko Haram school attack". Yahoo News. Retrieved 6 March 2014.
- ↑ "Nigeria children killed and school razed". Al Jazeera. 25 Feb 2014. Retrieved 6 March 2014.