Ibrahim Shema

Ɗan siyasar Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Katsina
(an turo daga Ibrahim Shehu Shema)

ä

Mukala mai kyau
Ibrahim Shema
gwamnan jihar Katsina

29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015
Umaru Musa Yar'Adua - Aminu Bello Masari
Rayuwa
Haihuwa Dass (Nijeriya), 22 Satumba 1952 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Barista Ibrahim Shehu ShemaAbout this soundIbrahim Shehu Shema  (An haife shi ranar 22 ga watan Satumba, shekara ta alif dari tara da hamsin da bakwai (1957) miladiyya. Lauya ne kuma ɗan siyasa ɗan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Katsina da ke a arewa maso yammacin ƙasar a lokacin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2007.[1]

Ibrahim Shema

An sake zaben shi na tsawon shekaru hudu a ranar 28 ga watan Afrilu, shekarar 2011, wanda ya yi dukkan takarar a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).[2] Wa’adinsa na biyu a kan karagar mulkin gwamnan jihar na shekaru hudu ya Kare ne, a ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2015, daga nan ya mikawa Aminu Bello Masari zaɓaɓɓen gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress Mulki biyo bayan sabon babban zaben kasar na shekarata2015.

Rayuwar farko da Ilimi

gyara sashe

An haifi Ibrahim Shema a ranar 22 ga watan Satumba a shekara ta 1957 a garin Dutsin-Ma da ke matsayin ƙaramar hukuma a jihar Katsina.

Ya halarci Makarantar Firamare ta Nasarawa, Katsina (1964-1971) da Makarantar Sakandaren Gwamnati, Kafanchan (1972-1976). Ya yi karatu a Kwalejin Arts, Science & Technology, Zariya daga shekara ta 1977 zuwa 1980, ya samu adimishan a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya kammala karatun digiri na biyu (LLB) a shekarar 1983. Bayan shekara ɗaya ya samu B.L a Nigerian Law School, Victoria Island, Lagos. A lokacin da yake aikin lauya, ya yi karatun digiri na biyu a fannin kasuwanci a Jami'ar Ahmadu Bello, inda ya kammala a shekarar 1998.[1]

Ibrahim shehu ya kasance babban Lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari'a na jihar (Agusta 1999 - Mayu 2003) a lokacin da Umaru Musa Yar'adua ya ke a matsayin gwamnan jihar Katsina na farko. Daga nan kuma ya koma aikinsa na sirri a Kaduna. A watan Janairun shekarar 2005, an nada shi memba na kwamitin musamman na jam’iyyar PDP kan rikicin Anambra. Sannan ya rike mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa ( shiyyar Arewa maso Yamma) (Satumba 2005 – Nuwamba 2006). A lokaci guda kuma, Ibrahim shema ya zama shugaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar PDP na kasa, kuma shugaban majalisar gudanarwa, Cibiyar Jam’iyyar PDPn.

 
Ibrahim Shema tare da ɗan shi

Ibrahim Shema ya taba zama shugaban kwamitin sulhu na kasa na jam'iyyar PDP ta Kudu maso Kudu (Mayu zuwa Yuni 2006). Ya kuma rike mukamin Shugaban Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) daga watan Disamba shekarar ta 2005 zuwa Nuwamban shekarar 2006, a lokacin da ya lashe tikitin jam'iyyar PDP na tsayawa takarar gwamna a jihar Katsina a shekara ta 2007.

Gwamnan jihar Katsina

gyara sashe
 
Jihar Katsina a cikin Taswirar kasar ta ta Najeriya da launin Ja-ja-jir

An zaɓi Ibrahim Shehu Shema a matsayin Gwamnan jihar Katsina a ranar 12 ga watan Afrilun shekara ta 2007, inda Ya gaji Marigayi Umaru Yar’adua mai barin mulki, wanda daga bisani shi kuma aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa. Ya hau karagar mulki ne a ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2007. An bayyana Shema a matsayin “gwamna mai rowa,” saboda kin buɗe rumfunan jihar Katsina ga Yan siyasar Katsina, yanayin da yake da alaƙa da tsohon gwamnan jihar, Umaru Musa Yar'adua.[3]

Karo na biyu

gyara sashe
 
Ibrahim Shema a cikin gwamnoni

An sake zaben Ibrahim Shema na tsawon wasu shekaru hudun a ranar 28 ga watan Afrilun shekara ta 2011, inda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP). Shema ya samu kuri’u miliyan daya da dubu ashirin da bakwai da dari tara da sha biyu (1,027,912) sai Aminu Masari na jam’iyyar Congress for Progressive Change CPC, da ƙuri’u 555,769. Ɗan takarar jam'iyar Action Congress of Nigeria (ACN) ya zo na uku da kuri’u 19,990[2].

Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Katsina, Tasiu Umar Mashi, ya rasu a watan Nuwamba shekarar 2009, a ofishin kwamishinan Yan sandan jihar Katsina, Danazumi Doma. Takaddama game da lamarin da ya kai ga mutuwarsa ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ɓangarorin PDP da ke adawa da Shema, ɗaya kuma ƙarƙashin jagorancin ministan noma da albarkatun ruwa, Dr. Abba Sayyadi Ruma. A watan Disambar shekara ta 2010, Shema ya sake lashe zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, a fafatawar da shi kaɗai ne ɗan takara.[4]

Ya auri Fatima Ibrahim Shema, su na da ƴaƴa huɗu, maza ukku (3) mace ɗaya (1), ya Kuma auri Maryam yar adua , yada da alhaji Kabir shema.[5]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Governor Ibrahim Shehu Shema of Katsina". Nigeria Governors Forum. Retrieved 2009-12-13.
  2. 2.0 2.1 "Guber Polls - PDP Shocks the North https://allafrica.com/stories/201104280233.html. Leadership. 28 April 2011. Retrieved 30 April 2011.
  3. ISMAIL OMIPIDAN (23 August 2009). "North -West 2011: The storm gathers". Daily Sun. Archived from the original on 26 September 2009. Retrieved 2009-12-13.
  4. Imam Imam (24 November 2009). "In Katsina, Tasiu's Death Sparks Off Controversy". ThisDay. Retrieved 2009-12-13.
  5. https://dailytrust.com/tag/ibrahim-shema/