Hari a Kaduna da Abuja, Yuni 2014

Jerin hare-haren a tsakkiyar Najeriya

A tsakanin ranakun 23 zuwa 25 ga watan yunin shekarar 2014, an kai wasu hare-hare a tsakiyar Najeriya. A ranakun 23-24 ga watan Yuni, wasu ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan jihar Kaduna, inda suka kashe mutane kusan 150. An ɗora alhakin kai harin kan ƴan ƙabilar Fulani. A ranar 25 ga watan Yunin 2014, wani bam ya tashi a Emab Plaza dake babban birnin tarayya Abuja, inda ya kashe aƙalla mutane 21. Dangane da harin bam din, sojojin Najeriya sun kai farmaki kan sansanonin 'yan bindiga biyu a ranar 26 ga watan Yuni, inda suka kashe fiye da mutane 100.

Infotaula d'esdevenimentHari a Kaduna da Abuja, Yuni 2014
Map
 9°04′00″N 7°29′00″E / 9.0667°N 7.4833°E / 9.0667; 7.4833
Iri aukuwa
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 25 ga Yuni, 2014
Wuri Abuja
Adadin waɗanda suka rasu 22
Adadin waɗanda suka samu raunuka 17

Wai-wa-ye

gyara sashe

Sama da mutane 20,000 ne aka kashe a Najeriya tsakanin shekarar 2009 zuwa 2014 a hare-haren da ƴan ta'addar Boko Haram ke jagoranta.[1] Ƙungiyar Boko Haram dai na adawa da mayar da Najeriya zuwa kasashen Yamma, wanda suke ganin shi ne ummul haba'isin aikata laifuka a ƙasar.[2] Gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta ɓaci a cikin watan Mayun 2013 a jihar Borno a yaƙin da take yi da masu tada ƙayar bayan.[3] Sakamakon murƙushe ƴan ta’addan, ya kasa daidaita ƙasar.[4][5]

Hare-haren mayaƙan Boko Haram sun ƙara tsananta a shekarar 2014. A watan Fabrairu, ƙungiyar ta kashe Kiristoci fiye da 100 a ƙauyukan Doron Baga da Izghe.[4] Haka kuma a cikin watan Fabrairu, an kashe yara maza 59 a harin da aka kai a Kwalejin Gwamnatin Tarayya a Jihar Yobe.[6]

A tsakiyar watan Afrilu, an zargin ƙungiyar Boko Haram da haddasa mutuwar mutane kusan 4,000 a shekarar 2014.[4] Daga nan ne ƴan bindiga suka kai hari wata makaranta suka yi garkuwa da ƴan mata 276, waɗanda 57 daga cikinsu suka tsere a garin Chibok. Lamarin ya jawo hankalin duniya kan halin da ake ciki a Najeriya, kuma ƙasashen yammacin duniya sun yi alƙawarin taimakawa wajen yakar ƴan ƙungiyar Boko Haram. Sai dai an ci gaba da kai hare-hare.[7] A ranar 20 ga watan Mayu, an kashe mutane 118 a wani harin bam da aka kai a birnin Jos. Washegari, an kashe mutane goma sha biyu a wani samame da aka kai wani ƙauye.[8] Daga baya ƙungiyoyin ƴan banga sun kafu a ko’ina a Arewa, tare da samun nasarar daƙile wasu hare-haren.[9]

Hare-haren da aka kai a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno na da wuya a iya tabbatar da su saboda rashin kyawun ingantattun hanyoyin sadarwa.[10]

Har ila yau, Najeriya na fuskantar hare-hare daga ƙungiyar MEND.

Hari a ƙauyukan Kaduna

gyara sashe

A ranar 23 ga watan Yunin 2014, wasu ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Kabamu da Ankpong a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 38 a cewar shugaban ƴan banga, Christopher Chisom.[11] Gwamna Ramalan Yero, ya tabbatar da faruwar harin, kodayake rahotanni sun ce ƙauyukan sun kai harin kamar Fadan Karshi da Nandu. Ya ce an kashe mutanen ƙauyen 17 da misalin karfe 10 na dare a Fadan Karshi, tare da kama ko kashe mahara biyu. Da karfe 2 na safe wasu ‘yan bindigar kuma sun kashe mutane 21 a Nandu. “Da yawa” wasu kuma sun sami raunuka, kodayake ba a samu takamaiman adadi ba. Shugaban ƙungiyar ta (Ninzon Progressive Youths Organisation) ya ce wata wasiƙar barazana daga Fulani ta yi gargaɗi kai harin a farkon watan.[12]

Ƙauyuka bakwai

gyara sashe

A yammacin wannan rana, wasu ƴan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka guda bakwai: Dogon-Daji, Gani, Hayin-Kwanta, Kabani, Kabamu, Kobin, da Naidu. A cewar Chisom, an kashe ƙarin wasu mutane 123 a harin da aka kai cikin dare: 38 a Kobin, 30 a Kabamu, 21 a Dogon-Daji, 16 a Naidu, 9 a Gani, 5 a Hayin Kwanta, 4 a Kabani.[11] Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN, ta kuma ruwaito cewa an kashe aƙalla mutane 100 a hare-haren. Rahotanni sun ce biyu daga cikin maharan suna sanye da kakin ƴan sanda.[13] Ba a fitar da adaɗin waɗanda suka mutu a hukumance ba.[11]

Ba a dai san ko su waye waɗanda suka kai harin ba, duk da cewa an kama wasu Fulani makiyaya guda uku a harin da aka kai ranar 25 ga watan Yuni. Mai magana da yawun ƙungiyar ta CAN ya ce "Na yi imanin cewa su 'yan ta'adda ne saboda Fulanin da muke rayuwa da su ba za su iya yin wannan abu ba."[13] Ya kuma ce wannan ya nuna cewa addini ne ya sa aka kai harin. An kuma samu bindiga ƙirar AK-47 guda uku da alburusai 158 a kamen. [13] Karamar hukumar Sanga ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 sakamakon hare-haren.[11]

Harin bom a Emab Plaza

gyara sashe

Wani abin fashewa ya fashe a Emab Plaza, cibiyar hada-hadar kasuwanci da ke birnin tarayya Abuja da misalin karfe 16:00 na ranar 25 ga watan Yuni kusa da ofisoshin gwamnatin tarayya.[14][15] Fashewar wadda ta faru a lokacin da ake yawan samun cunkoso, ya haifar da hayaki mai yawa. Wani ganau ya ruwaito cewa: “Mun ji wata babbar hayaniya kuma ginin ya girgiza . . . Mun ga hayaki da mutane cikin jini. Hargitsi ne kawai."[14] A cewar rahotannin hukuma, an kashe aƙalla mutane 21 a harin. Jaridar Premium Times ta ruwaito an samu mutuwar mutane aƙalla 30 tare da yiyuwar samun karin wasu adadin.[15] Sama da mutane 50 ne suka jikkata a harin.[16]

An harbe wanda ake zargi da yunƙurin tserewa daga wurin. Wata jaka da yake ɗauke da ita na ɗauke da ƙarin wasu bama-bamai acikin jakar. A ranar 26 ga watan Yuni, rundunar hadin gwiwa ta ƙasa da ƙasa ta mayar da martani kan harin ta hanyar kai farmaki kan sansanonin ‘yan bindiga guda biyu. A cewar Ministan Tsaro, an kashe kusan mayaƙan 50 a kowane wuri. Sojoji biyu ne aka kashe a samamen.[16] Shugaba Goodluck Jonathan ya dakatar da taron Kungiyar Tarayyar Afirka domin ganawa da iyalan waɗanda fashewar ta shafa a ranar 27 ga watan Yuni. “’Yan Najeriya suna fafutuka, suna tunanin yadda za su bayar da tasu gudummawar ga ci gaban [al’umma] kuma suna aiki tukuru don kula da iyalansu [yayin da] wasu ke shagaltuwa da kashe mutane,” in ji shi.[17]

Ba a ɗauki alhakin kai harin ba, amma rahotannin kafafen yaɗa labarai gaba ɗaya na alaƙanta tashin bam din da ƙungiyar Boko Haram.[14][15] Mako guda kafin hakan, bayanan sirri na gwamnati sun nuna cewa ƙungiyar na shirin yin awon gaba da manyan motocin dakon mai tare da kai su cikin babban birnin ƙasar, waɗanda ke maƙare fam da bama-bamai.[16]

Manazarta

gyara sashe
  1. Marius Pricopi (2016). "Tactics Used by the Terrorist Organisation Boko Haram". Buletin Stiintific. Missing or empty |url= (help)
  2. McElroy, Damien (6 July 2013). "Extremist attack in Nigeria kills 42 at boarding school". The Daily Telegraph. Retrieved 3 October 2013.
  3. "Nigeria school attack claims 42 lives". The Australian. Agence France-Presse. 6 July 2013. Retrieved 3 October 2013.
  4. 4.0 4.1 4.2 Dorell, Oren (21 April 2014). "Terrorists kidnap more than 200 Nigerian girls". USA Today. Retrieved 23 April 2014.
  5. Aronson, Samuel (28 April 2014). "AQIM and Boko Haram Threats to Western Interests in the Africa's Sahel". Combating Terrorism Center Sentinel (CTC), West Point. Archived from the original on 13 May 2014. Retrieved 27 January 2023.
  6. "Boko Haram kills 59 children at Nigerian boarding school". The Guardian. 25 February 2014. Archived from the original on 26 February 2014. Retrieved 6 March 2014.
  7. "Bombing at northeast Nigeria football match kills at least 40". The Times of India. Agence France-Presse. 2 June 2014. Retrieved 3 June 2014.
  8. "Nigeria violence: 'Boko Haram' kill 27 in village attacks". BBC. 21 May 2014. Retrieved 21 May 2014.
  9. "Witnesses: Extremists abduct 91 more people in Nigeria in deadly weekend attacks on villages". Fox News Channel. Associated Press. 24 June 2014. Retrieved 25 June 2014.
  10. Hamza Idris (2014-06-23). "allAfrica.com: Nigeria: Three Soldiers Feared Killed As Bomber Hits Military Post". Daily Trust - AllAfrica. Retrieved 2014-06-28.
  11. 11.0 11.1 11.2 11.3 John Shiklam (25 June 2014). "Nigeria: Kaduna – Suspected Fulani Herdsmen Kill 123 in Fresh Attacks". This Day. All Africa. Retrieved 27 June 2014.
  12. "Nigeria: Fulani Attack Kaduna Villages, Kill 38". Vanguard. All Africa. 25 June 2014. Retrieved 27 June 2014.
  13. 13.0 13.1 13.2 "Nigeria: 100 Killed in Kaduna Village Attack". The Daily Independent. All Africa. 25 June 2014. Retrieved 27 June 2014.
  14. 14.0 14.1 14.2 "Bomb killed 21 people in Abuja". BBC News. 25 June 2014. Retrieved 26 June 2014.
  15. 15.0 15.1 15.2 "Deadly shopping mall explosion in Nigeria". DW. AP, AFP, DPA, Reuters. 25 June 2014. Retrieved 26 June 2014.
  16. 16.0 16.1 16.2 Elisha Bala-Gbogbo; Daniel Magnowski (27 June 2014). "Nigeria Militant Camps Raided After Abuja Bombing Killed 21". Bloomberg. Retrieved 27 June 2014.
  17. "Fear grips Nigeria capital after attack". Sky News. 27 June 2014. Archived from the original on 27 June 2014. Retrieved 27 June 2014.

Coordinates: 9°04′00″N 7°29′00″E / 9.0667°N 7.4833°E / 9.0667; 7.4833