Premium Times
Premium Times jarida ce ta yanar gizo a Najeriya da ke Abuja a babban birnin tarayya. An ƙaddamar da ita a cikin shekarar 2011.[1] Jaridar sananna ce akan bincike da ma samar da rahotanni.
Premium Times | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Iri | takardar jarida |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Mulki | |
Hedkwata | Abuja |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2011 |
Kyaututtuka da zaɓe
gyara sasheA shekarar 2013, an zaɓi jaridar Premium Times a matsayin Website/blog of the year a lambar yabo ta Nigerian Broadcasters Merit Award.[2] A cikin shekara ta 2017, 'yan jarida na Premium Times sun samu kyautar the Pulitzer Prize, biyo bayan haɗin gwiwar su da ƙasa da ƙasa wurin bincike akan Takardun Panama, wanda ya nuna cin hanci da rashawa a wuraren haraji na teku da mutane da yawa ke amfani da su.[3] A watan Nuwamba 2017, ƙungiyar (Global Investigative Journalism Network) ta sanar da cewa jaridar Premium Times ta samu lambar yabo ta (Global Shining Light Award) saboda aikin binciken kisan gilla da aka yi a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da kuma yadda aka kitsa kisan kiyashin Onitsha da magoya bayan Biafra su kayi.[4]
Duba kuma
gyara sashe* Mujalla
Manazarta
gyara sashe- ↑ "About Us". Premium Times. Retrieved 22 April 2018.
- ↑ "Here are the Nominees for Nigerian Broadcasters Merit Awards 2013". Olori Supergal (in Turanci). 31 October 2013. Archived from the original on 19 April 2019. Retrieved 11 April 2018.
- ↑ Digit, Control (April 11, 2017). "'Fake News' reporters win Pulitzer awards". Business Day Newspaper. Business Day Newspaper. Archived from the original on May 24, 2018. Retrieved 24 May 2018.
- ↑ GIJN, Staff. "Investigative Stories from Iraq, Nigeria Win Global Shining Light Award". Global Investigative Journalism Network. Global Investigative Journalism Network. Retrieved 24 May 2018.