Hanafiyya

Mazahabar hannafiya, daya daga cikin mazahabobi guda hudu na sunna

Mazhabar Hanafiyya (larabci|حنفي) (Ḥanafī) tana daya daga cikin manyan Mazhabobi guda hudu wadanda addinin musulunci ke dasu, wurin karantar da Sunnar manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, Dan yin hukunce hukuncen (fiqhu).[1] ita ma dai Mazhabar ta samu sunanta ne daga sunan Babban Malaminta, wanda makarantarsa ce ake wa Mazhabar lakabi da shi, wato Alshaykh Imam Abū Ḥanīfa an-Nu‘man ibn Thābit, ya rasu a shekarar (d. 767),shi Tabi‘i ne, kuma dokokin akidarsa an samo su ne ta hanyar kiyayewar manyan Daliban sa da suka yi, Abu Yusuf da Muhammad al-Shaybani. Manyan Mazhabobin addinin musulunci daman da sune wadannan hudun da suka shahara, wato; Malikiyya, Shafi`iyya da Hanbaliya.[2][3].

Hanafiyya
Mai kafa gindi Imam Abu Hanifa
Classification
Sunan asali المذهب الحنفي
Majmaʻ al-baḥrayn wa-multaqá al-nayyirayn
Hazrat Allama Mufti Syed Faheem Ahmed Shah
Taswirar kasar musulunci

Mazhabar Hanafiyya ita ce Mazhabar da ke da mafi yawan mabiya a tsakanin musulmai masu bin Sunnah a duk fadin duniya.[4] ita ce ake bi a kasashen da suka taba kasancewa karkashin mulkin daular usmaniyya (Ottoman Empire), da daular Mughal da masarautun shugabannin Turkic da ke Indian subcontinent, northwest China da Central Asia. A yanzu ana bin Mazhabar Hanafiyya a kasashe da yankuna kamar: Turkiya, da Balkans, Syria, Lebanon, Jordan, Palestine, Misra, wasu bangaren kasashen Iraki da Iran, bangaren Rasha, Turkmenistan, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan, Uzbekistan, Afghanistan, Pakistan, bangaren Indiya da China, da Bangladesh.[4][5][6]

A matsayin khalifah na hudu, Ali ya canja birnin musulunci zuwa Kufa, kuma yawancin first generation musulmai sun koma nan da zama, makarantar dokokin Hanafiyya ta sanya yawancin shari'unta a kan bin abubuwan da Sahabban farko suka zo da su wadanda ke zama a Iraq. Dukda, daga baya Hanafiyya anfara kiranta da Kufa ko Iraqi school a Lokacin. Ali da Abdullah, dan Masud su suka samar da asalin farkon makarantar, tareda wasu mutane kamar Muhammad al-Baqir, Ja'far al-Sadiq,da Zayd ibn Ali. Many jurists da historians sun rayu a Kufa har daya daga cikin manyan Malaman Abu Hanifa, wato Hammad ibn Sulayman.

A farkon tarihin musulunci, Hanafi doctrine ba a taskance ta ba. Saidai fiqhu an tattara shi da taskance shi a karni na 11th.[7] Shugabannin Turkiya sune suka fara amfani da fiqhun Hanafiyya , suka yarda da shi akan traditionalist Medina-based fiqhs which favored correlating all laws to Quran and Hadiths and disfavored Islamic law based on discretion of jurists.[8] YAN Abbasids patronized the Hanafi school from the 10th century onwards. The Seljuk Turkish dynasties of 11th and 12th centuries, followed by Ottomans adopted Hanafi fiqh. Fadadar Turkawa ya sa suka yada fiqhun Hanafiyya a cikin tsakiyar Asiya zuwa kudancin Asiya da kuma kafa Daular Seljuk, Timurid dynasty,Khanates da Delhi Sultanate.[7][8].

Manazarta

gyara sashe
  1. Hisham M. Ramadan (2006), Understanding Islamic Law: From Classical to Contemporary, Rowman Altamira, ISBN|978-0759109919, pp. 24–29
  2. Gregory Mack, Jurisprudence, in Gerhard Böwering et al (2012), The Princeton Encyclopedia of Islamic Political Thought, Princeton University Press, ISBN|978-0691134840, p. 289
  3. Sunnite Encyclopædia Britannica (2014)
  4. 4.0 4.1 Jurisprudence and Law – Islam Reorienting the Veil, University of North Carolina (2009)
  5. Siegbert Uhlig (2005), "Hanafism" in Encyclopaedia Aethiopica: D-Ha, Vol 2, Otto Harrassowitz Verlag, ISBN|978-3447052382, pp. 997–99
  6. Abu Umar Faruq Ahmad (2010), Theory and Practice of Modern Islamic Finance, ISBN|978-1599425177, pp. 77–78
  7. 7.0 7.1 Nazeer Ahmed, Islam in Global History, ISBN|978-0738859620, pp. 112–14
  8. 8.0 8.1 John L. Esposito (1999), The Oxford History of Islam, Oxford University Press, 08033994793.ABA, pp. 112–14