Fati Nijar
Binta Labaran (wacce aka fi sani da Fati Nijar) ƴar ƙasar Nijar mawaƙiya ce kuma jarumar da ta samu laƙabin "Gimbiyar Mawaƙan Hausa" (wanda aka fassara zuwa "Princess of Hausa Music " ). An haife ta kuma ta girma a garin Maraɗi na ƙasar Nijar inda kuma ta yi karatun Al-Qur'ani kafin ta wuce Najeriya don ci gaba da sana'ar waƙa. Fati Nijar ta fito da albam 4 masu waƙoƙi sama da 500. Ita ‘yar ƙabilar Hausa ce.[1][2][3]
Fati Niger | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | mace |
Ƙasar asali | Nijar |
Sunan haihuwa | Binta Labaran |
Suna | Binta (mul) |
Sunan dangi | Niger |
Wurin haihuwa | Maradi |
Harsuna | Hausa |
Sana'a | mawaƙi, jarumi da mai tsara fim |
Work period (start) (en) | 2004 |
Rayuwar farko da aiki
gyara sasheAn haifi Fati Nijar kuma ta girma a Maraɗi, Nijar. Ta kasance tana da sha’awar rera waƙa musamman waƙoƙin Hausa na gargajiya waɗanda galibi ake rera su a cikin daren wata a tsakanin matasa a ƙauyukan Hausa.
Bayan ta ziyarci 'yar uwarta a shekarar 2004 a Najeriya, ta gano masana'antar waƙa da ta bunƙasa a cikin birnin Kano. A nan ta nemi shawarar yayarta da yardarta kafin ta ɗauki wakar ta ta farko a ɗakin taro na Ali Baba da ke cikin birnin Kano.[4]
Waƙa
gyara sasheFati ta fitar da kundin waƙa 4 da kuma waƙoƙi sama da 500. Ta kuma fito a fina-finan Hausa na Kannywood daban-daban.[5][6]
Waƙoƙi
gyara sasheFati Nijar, ta yi fice a waƙoƙin fim masu yawan gaske, dama na siyasa gami da bukukuwa. To amma waƙar ta ta ‘Girma-Girma’, ta ɗaga darajar ta inda ta shahara kuma aka santa a duniya.[7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.blueprint.ng/why-im-still-single-fati-niger/
- ↑ https://dailytrust.com/fati-niger-an-exotic-songbird-from-niger-rep/
- ↑ https://dailytrust.com/5-kannywood-divas-that-are-not-nigerians/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-05-18. Retrieved 2023-03-08.
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-51531594.amp
- ↑ https://www.afro.who.int/news/who-partners-fati-niger-popular-nigerian-based-singer-create-awareness-cholera-meningitis-and
- ↑ https://fimmagazine.com/fati-nijar-buri-na-in-sha-gaban-duk-wata-jaruma/