Dabo Aliyu CON mni psc (29 ga watan Disambar 1947[ana buƙatar hujja] – 13 ga watan Disambar 2020) ya kasance shugaban riƙo na jihar Anambra daga Nuwamba zuwa Disambar 1993, kuma ya riƙe muƙamin Administrator na jihar Yobe daga Disambar 1993 zuwa Agustan 1996 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha. Ya taɓa zama mataimakin darakta NSO Annex State House, Ya kuma kasance Mataimakin Sufeto Janar na ƴan sanda mai kula da shiyya ta 7 Abuja. An ba shi lambar yabo kan rigakafin laifuka, lambar yabo ga mafi kyawun kwamishinan ƴan sanda daga babban sufeton ƴan sanda da kuma bayar da kyautar mafi kyawun aikin ƴan sanda a jihar Anambra. Ya yi zama a Jihar Kaduna, kuma shi ne Sardaunan Ruma, sarauta a garinsa, Ruma.[1]

Dabo Aliyu
gwamnan jihar Yobe

9 Disamba 1993 - 22 ga Augusta, 1996
Bukar Ibrahim - John Ben Kalio (en) Fassara
Gwamnan jahar Anambra

Nuwamba, 1993 - Disamba 1993
Chukwuemeka Ezeife - Mike Attah
Rayuwa
Cikakken suna Dabo Aliyu
Haihuwa Batsari, 29 Disamba 1947
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 13 Disamba 2020
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

An kawo rahoto cewa Aliyu ya rasu a Kaduna a ranar 13 ga Disambar 2020, bayan rashin lafiya da ba a bayyana ba.[2][3]

Manazarta

gyara sashe