Arewa ta tsakiya (wanda aka fi sani da Arewa-Tsakiya ) na daya daga cikin shiyyoyin siyasa shida na Najeriya wacce ke wakiltar mafi akasarin yankin tsakiyar kasar. Ta ƙunshi jihohi shida - Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Plateau - da kuma babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Arewa ta Tsakiya
Bayanai
Suna a hukumance
North- central Zone
Iri administrative territorial entity (en) Fassara
Ƙasa Najeriya

Yankin Arewa ta tsakiya ta mamaye fadin kasar baki daya, tun daga kan iyakar kasar da Kamaru zuwa na Benin. Dangane da mahalli, yankin ta mamaye gandun daji na Guinea-savanna mosaic, tare da ɓangaren yamma ta faɗo cikin yankin savanna na yammacin Sudan. Jihar Filato kuma ana kiranta da sunan Jos Plateau, wacce ke daidai tsakiyar yankin gabas ta tsakiya.

Yankin tana da yawan mutane kimanin miliyan 20, kusan kashi 11% na yawan al'ummar Najeriya. Babban birnin kasar Abuja, dake cikin babban birnin tarayya, da kuma Ilorin da Jos, sune biranen da suka fi yawan jama'a a yankin Arewa ta tsakiya, haka zalika kuma birnen yankin sune na shida, na bakwai da na takwas mafi yawan mutane a Najeriya.

Manazarta

gyara sashe