Aliyu Kama

Dan Siyasa Kuma tsohon Soja a Najeriya

Aliyu Adu Umar Kama wanda aka fi sani da Aliyu Kama (an haife shi a 15 ga watan Yuli,1949)[1] ya kasance gwamna a jahar Plateau (jiha), Najeriya daga watan Yulin shekarar 1988 zuwa watan Agusta 1990 a lokacin mulkin soja na janar Ibrahim Babangida .

Aliyu Kama
gwamnan jihar Filato

ga Yuli, 1988 - ga Augusta, 1990
Lawrence Onoja - Joshua Madaki
Rayuwa
Haihuwa 15 ga Yuni, 1949 (75 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar

Farkon rayuwa da ilimi

gyara sashe

An haifi Aliyu Kama a karamar hukumar Hong (Nijeriya) , a jihar Adamawa dan asalin kabilan Kilba. Ya halarci Makarantar sakandari ta Gwamnati dake, Yola ta Arewa (1693-1968), ya kuma halarci makarantar horar da sojoji dake Kaduna (jiha) (1969-1972) da Army School of supply and transport, Ibadan, (1972).[2]

Kama ya kasance dan takarar gwamna a Jihar Adamawa, Karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zaɓen shekarar 2007. [3] A shekara ta 2009 yana daga cikin masu neman a samar da jihar Amana da za'a cira daga jihar Adamawa.[4] A watan Yuli shekarar 2009, ya kasance Ciyaman na hukumar board of Federal Superphosphate Fertilizer company, Kaduna.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.bing.com/ck/a?!&&p=a65e826d95ea182aJmltdHM9MTcxOTEwMDgwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTIwNg&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Aliyu+Adu+Umar+Kama&u=a1aHR0cHM6Ly93d3cuYmlvZ3JhcGhpZXMubmV0L2Jpb2dyYXBoeS9hbGl5dS1rYW1hL20vMGMwMDdjbA&ntb=1
  2. Sen Luka Gwom Zangabadt (1993). Plateau State political and administrative system: a historical analysis. Fab Education Books. p. 16. ISBN 978-2023-97-3.
  3. Umar Yusuf (21 December 2005). "2007: PDP Assures 13 Guber Aspirants of Equal Treatment in Adamawa". Vanguard. Retrieved 30 May 2010.
  4. Edward Wabundani (7 January 2009). "Amana - a State Based On Trust". Daily Trust. Retrieved 30 May 2010.
  5. Yunus Abdulhamid (25 June 2009). "FG orders N6bn worth of fertilizer from FSFC". Daily Trust. Retrieved 30 May 2010. [dead link]